Kasashe 70 na taro kan Isra'ila a Paris

Masu macin neman zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Rabon da a yi wata tattaunawa tsakanin Isra'ila da Falasdinawa tun shekara ta 2014

Wani taro na kasa-da-kasa domin kokarin sake soma tattaunawar kawo zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa na kankama a Paris babban birnin kasar Faransa.

Ministocin harkokin waje da jami'an diflomasiyya daga kasashe kimanin 70 na ci gaba da isa babban birnin na Faransa inda ake sa ran su sake jaddada goyon bayansu ga kafa kasar Falasdinu a zaman hanyar warware rikicin.

Falasdinawa dai sun yi maraba da zuwan wannan taron amma Isra'ila wadda ta ki tura wakilinta, ta ce an tsara taron ne domin yi ma ta sakiyar da ba ruwa.

Da ma dai an gayyaci bangarorin biyu ne domin su ji matsayar da taron zai cimma kawai; amma ba don su shiga cikin shawarwarin da za a yi ba.

Tankiya

Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu wata tankiya tsakanin Isra'ila da kasashen duniya a watan jiya bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wani kudurin da ke yin tir da yadda ta ke ci gaba da giggina matsgunan yahudawa a yankunan Falasdinawa da ta mamaye.

Isra'ila dai ta zargi gwamnatin Obama da kitsa wannan kudurin ta bayan fage da kuma bayar da damar amince wa da shi ta hanyar kin amfani da ikonta na hawan kujerar-na-ki a kwamitin tsaro; amma fadar White House ta musanta wannan zargin.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce Sakataren harkokin wajen kasar John Kerry zai halarci taron domin tabbatar duk abin da aka yi a wajen ''ya yi ma'ana kuma ya yi wa kowane bangare dadi.''