Kocin Chelsea ya ce bai san ranar da Costa zai koma buga kwallo ba

Chelsea striker Diego Costa (left) and manager Antonio Conte

Asalin hoton, AP

Kocin Chelsea Antonio Conte ya ce ba shi da tabbas kan ranar da dan wasan kulob din Diego Costa zai gama jinya tunda ba a sanya shi a wasan da suka doke Leicester da ci 3-0 ba.

Costa dai ya yi ta ja-in-ja da kocin a kan dacewar sa ta buga wasa bayan Conte ya ce dan wasan dan kasar Spain ya yi korafin cewa yana fama da ciwon baya ranar Talata.

Wasu rahotanni na cewa dan wasan na shirin komawa China.

Sai dai Conte ya ce, "Ban san tsawon lokacin da zai kwashe yana jinya ba. Ba ni nake jin radadin da yake ji ba. Za mu tattauna a kan hakan a makon gobe."

Costa ya taba muhimmiyar rawa a nasarar da kulob din yake samu a kakar gasar Premier ta bana, inda ya zura kwallo 14 sannan ya taimaka aka zura kwallo biyar.

Wani mai yi wa BBC sharhi kan wasanni Ian Wright ya ce: "Fitar da Costa daga wasa a wannan lokacin da ake matukar bukatar sa abin mamaki ne. Ya zura kwallon 14 a kakar wasa ta bana don haka ana bukatar dan wasa kamar sa. Ina ganin kulob din na neman yin saki-na-dafe."