An aiwatar da hukuncin kisa kan 'yan Shi'a a Bahrain

'Yan Shi'a

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan Shi'a sun sha yin zanga-zangar kyamar gwamnatin Bahrain

Hukumomi a kasar Bahrain sun zartar da hukuncin kisa kan wasu 'yan Shi'a masu fafutika uku wadanda aka samu da laifin kisan wasu 'yan sanda ta hanyar kai musu harin bam a shekarar 2014.

Wannan ne karon farko da kasar ta Bahrain da ke bin mazaharin Sunnah ta aiwatar da hukuncin kisa kan fursunoni cikin shekara shida da suka wuce.

Babbar kotun kasar ce ta tabbatar da hukuncin kisan a makon jiya.

Daruruwan mutane ne suka yi zanga-zanga a kan titunan kasar ranar Asabar bayan rahotanni sun bayyana a shafukan zumunta cewa ana shirin kaddamar da hukuncin kisa kan mutanen ta hanyar harbi.

Ma'aikatar cikin gida ta kasar ta ce an kashe wani dan sanda yayin da aka jikkata wani dan sandan a lokacin zanga-zangar.

A shekarar 2011, musulmi mabiya Shi'a wadanda su ne tsiraru a kasar sun kaddamar da zanga-zanga sau da dama domin nuna bijirewar su ga gwamnatin kasar wacce jagororinta mabiya mazahabin Sunnah ne.