Barcelona ta kusa tarar da Real Madrid

Luis Suarez

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Luis Suarez ya zura kwallonsa ta 18 a bana

Luis Suarez ya zura kwallaye biyu a wasan da Barcelona ta buge cut Las Palmas da ci 5-0, abin da ya sa yanzu maki biyu ne kacal tsakanin ta Real Madrid a gasar cin kofin La Liga.

Suarez ya cafe kwallon da Andre Gomes ya buga inda ya cilla ta a ragar Palmas kafin hutun rabin lokaci, kuma daga nan ne Barca ta zura kwallaye uku rigis cikin kankanen lokaci bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Lionel Messi ya mika wa Suarez wata kwallon inda shi kuma ya bai wa Arda Turan wanda ya zura kwallo ta hudu.

Shi ma Aleix Vidal ya zura kwallonsa ta farko, bayan Paco Alcacer ya mika masa.

A wasu wasannin na La Liga na ranar Asabar, kwallon da Nicolas Gaitan ya zura a minti na takwas ta karfafa matsayin Atletico Madrid na hudu a saman teburin gasar bayan sun doke Real Betis 1-0, yayin da su kuma Athletic Bilbao suka tashi 0-0 da Leganes.

Messi na tsaka-mai-wuya?

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Lionel Messi ya ci kwallo a dukkan wasanni bakwai da ya buga wa Barcelona a jere

An dade ana rade-radin makomar Messi a Nou Camp, a yayin da babu wata cikakkiyar alama da ke nuna cewa za a tsawaita kwantaraginsa a kulob din ganin cewa a kakar wasa mai zuwa kwantaragin nasa zai kare.

Barca ta kori jami'in da ake gani shi ke jan-kafa a kokarin tsawaita kwantaragin dan kasar ta Argentina.

Pere Gratacos, shugaban hulda kan wasanni na kulob din, ya fada ranar Juma'a cewa sauran fitattun 'yan wasan kulob din ne suka sa Messi ya yi ficen da ake ganin ya yi.

Amma dukkan wannan hayaniya ba ta sanya Messi ya gaza a wasannin da yake yi ba, kasancewa ya ci gaba da jan zarensa.

Kasadar da Enrique ya yi

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Arda Turan ya zura kwallo ta hudu a wasan

Dole ne kulob din Barcelona ya ci wasan da ke gaban sa idan yana so ya kamo Real Madrid, ganin cewa ya rasa maki biyu a karawar da suka yi da Villareal inda suka tashi da ci 1-1 a makon jiya.

Kocin Barca Luis Enrique ya sani sarai cewa wannan makon na a-yi-ta-ta-kare ne saboda Real za ta fafata da Sevilla ranar Lahadi.

Amma duk da haka ya yi kasadar barin Andres Iniesta, Gerard Pique da kuma Neymar su huta domin tunkarar wasannin da za a yi nan gaba, ciki har da karawar da za su yi da Real Sociedad a gasar Copa del Rey mako biyu masu zuwa.