Zababben shugaban Gambia Adama Barrow zai zauna a Senegal

Buhari (Dama) na gaisawa da zababben shugaban Gambia Adama Barrow (Hagu), yayinda da shugaban Gambia mai barin gado Yahya Jammeh (Tsakiya) ke kallo

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto,

Mr Barrow (Hagu) da Mr Jammeh (Tsakiya) sun tattauna da shugaban Najeriya Buhari (Dama) a makon jiya

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya amince da karbar zababben shugaban Gambia Adama Barrow har ya zuwa lokacin rantsar da shi.

Shugabannin kasashen Afirka ta yamma ne suka bukaci hakan bayan taron kolin da suka gudanar a kasar Mali.

Shugaba Yahya Jammeh, wanda da farko ya amince da shan kaye a zaben, ya dawo ya ce ba zai sauka daga karagar mulkinsa ba har sai a cikin watan Mayu, lokacin kotun koli ta saurari kalubalantar da yake yi wa zaben.

Kungiyar ECOWAS ta bukaci kungiyar tarayyar Afirka AU ta amince da daukar matakin soji, muddin aka hana gudanar da bikin rantsar da Mr Barrow a ranar Alhamis.

A ranar Asabar ne shugabannin kasashen sun nanata kiran da suke yi ga Mr Jammeh ya sauka girma da arziki, a wani taron kasashen Afirka da Faransa a birnin Bamako.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Zababben shugaban Gambia Adama Barrow

Shugaban kasar Mali Ibrahim Keita ya yi kira ga a nuna dattaku irin na kasashen Afirka don kaucewa zub da jini, kana akwai fargabar cewa rashin sanin tabbas ka iya haifar da kwararar 'yan gudun hijira.

Dubban 'yan kasar Gambian ne, akasari mata da yara suka ketara kan iyaka zuwa Senegal makwabciyar kasar, ya zuwa kasar Guinea-Bissau inda ba sa bukatar takardar izinin zama, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Kungiyar tarayyar Afirka AU ta ce ba za ta ci gaba da daukar Mr Jammeh a matsayin shugaban kasa ba bayan karewar wa'adinsa.

Shugaba Jammeh mai shekara 51, ya karbi mulkin kasar a shekara ta 1994, kuma ana zarginsa da cin zarafin bil adama, duk kuwa da cewa ya gudanar da zabubbukan da aka saba yi.