An datse kawunan fursunoni 10 a tarzomar gidan yari a Brazil

Fursunoni a gidan yarin Alcacuz , birnin Natal

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An rika ganin fursunoni ta saman rufin kwanon gidan yarin Alcacuz

Fursunoni akalla 10 aka kashe a wata arangama tsakanin kungiyoyin 'yan daba a gidan yarin birnin Natal na kasar Brazil.

'Yan sanda sun ce sun shafe sa'oi 14 kafin su sake kwace iko da gidan yarin na Alcacuz.

"Ana ci gaba da gudanar da aikin tabbatar da tsaro, amma dai kura ta lafa'', kamar yadda kakakin 'yan sandan ya shaida wa BBC a Brazil.

Wannan ita ce zanga-zanga ta uku mafi muni a kasar ta Brazil cikin wannan shekarar.

Fursunoni kusan 100 ne suka mutu yayin zanga-zangar da aka gudanar a jihohin Amazonas da Roraima cikin farkon wannan watan.

An fara tashin hankali a gidan yarin Alcacuz a jihar Rio Grande Do Norte ne da yammacin ranar Asabar, lokacin da wasu kungiyoyin 'yan daba da ke wasu gidajen yarin kasar suka kai wa wasu kungiyoyin hari.

Ba a ba da rahoton tserewar fursunoni ba, kuma 'yan sanda sun ce adadin wadanda suka mutun ka iya karuwa.

Tashe-tashen hankula ba sabon abu ba ne a gidajen yarin kasar ta Brazil masu cunkoson jama'a, da akasari manyan kungigoyin 'yan daba ne ke iko da su.

Amma kuma karuwar tashe-tashen hankula a giadejn yarin cikin wannan shekarar ya sa matsin lamba kan shugaba Michel Temer na ya shawo kan matsalar.