Birtaniya: Da sake idan EU ta hana mu shiga kasuwannin bai-daya

Philip Hammond

Asalin hoton, EPA

Sakataren baitulmalin Birtaniya Philip Hammond ya gargadi kungiyar tarayyar turai EU cewa kasar za ta sauya tsarin tattalin arzikinta, muddin aka hana ta dama a kasuwannin bai-daya ba, bayan ta fice daga kungiyar.

Mr Hammond ya ce gwamnati ba za ta yi kwance ba, kuma za ta yi duk yadda za ta yi wajen cigaba da kasancewa gagara-gasa.

A na shi martanin Mr Jeremy Corbyn na jam'iyar Labour ya ce wannan wata alama ce ta fito-na-fito game da kasuwanci ta kasashen Turai.

A ranar Talata ne dai ake sa ran Pirai minista Theresa May za ta bayyana shirinta kan batun ficewar Birtaniyar daga kungiyar ta EU.

Wasu rahotanni sun ce za ta yi bayani kan ficewar Birtaniyar daga kasuwar kungiyar EU da kungiyar kwastan, ko da yake fadar ta ''Downing Street'' ta bayyana hakan da cewa ''shaci-fadi ne''.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Ana sa ran Theresa May za ta yi bayani kan a kawo karshen rarrabuwar kawuna kan batun ficewa daga kungiyar EU

A wata hira da jaridar kasar Jamus In Welt am Sonntag, Mr Hammond ya ce yana da tabbacin za a yi yarjejeniya kan damar kasuwancin.

" Amma kuma idan aka kai ka bango, dole kai ma ka zama wani abu daban'' Hammond ya kara fada.

" Muddin ba mu samu damar shiga kasuwannin kasashen Turai ba, muddin aka toshe mu, muddin Birtaniya fice daga kungiyar EU ba tare da wata yarjejeniya ba kan kasuwannin, to za mu shiga damuwa game da tattalin arzikinmu na dan wani lokaci''

" Ko da zai kasance a ce an tilasata mana daukar matakin sauya tsarin tattalin arzikinmu, Idole mu dawo da martabar gogayyar kasuwancinmu.