India: 'Sojoji su guji bayyana damuwarsu a shafukan intanet'

India

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Rundunar sojin India na gargadin jami'anta kan amfani da shafukan sada zumunta

Rundunar sojin kasar India ta gargadi sojojinta da su guji bayyana damuwarsu a shafukan sada zumunta.

Shugaban rundunar Janar Bipin Rawat ya ce za a hukunta duk wani jami'in sojin da ya aikata hakan.

Ya ce hakan na raunana gwiwar jami'an, kana rundunar sojin kasar na da nata tsarin yin gyara.

Kalaman na shi na zuwa ne bayan da aka nuna a wani faifen bidiyo daga saka a shafukan sada zumunta, wani jami'in soja na cewa wasu na gaba da shi sun tilasta masa wanke tsummokarai, da goge takalma, da kuma gwale-gwale.

An bada rahoton cewa manyan jami'an sun maida martani a wani faifen bidiyon cewa, mudddin sojoji suka cigaba da amfani da shafukan sada zumunta wajen bayyana damuwarsu, zai haifar da barazana ga batun da'a a aikin soja.