Daraktan hukumar CIA ta Amurka ya gargadi Trump da ya rage surutai

John Brennan - CIA

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Mr Brennan ya ce dole sai Mr Trump ya rage wallafa kalaman da ba su da tushe a shafinsa na Twitter

Daraktan hukumar leken asiri ta Amurka CIA John Brennan, ya gargadi zababben shugaba kasar Donald Trump ya kaucewa surutu maras ma'ana da zarar ya hau karagar mulki.

Ya ce yin hakan shi zai fi yiwa harkokin tsaron kasarsa alfanu.

An dai san Mr Trump da yawan banbarama wajen yin kalamai, kan batutuwan da suka shafi kasa a shafukansa na Twitter.

Mr Brennan ya kuma ce Mr Trump ya jahilci manufa da kuma abinda kasar Russia za ta iya aikatawa.

" Ina ga dole sai Mr Trump ya fahimci cewa maganganu a kan matakan da kasar Russia ta dauka a shekarun baya, wata hanya ce da ya kamata ya yi taka-tsan-tsan a kai'', in ji Brennan.

Kalaman na Mr Brennan wanda ya yi a wata hira da gidan talabijin na Fox News ranar Lahadi, na zuwa ne mako guda bayan fitar da wasu bayanan sirri na Amurka da ke cewa, akwai yiwuwar shugaban Russia President Vladimir Putin ya yi katsalandan a harkokin zaben shugaban kasa da aka gudanar a Amurkar.

Kremlin da tawagar Mr Trump su musanta rahotannin jaridar Times newspaper cewa duka bangarorin biyu na shirin gudanar da wani taro tsakanin Mr Trump da Mr Putin a Reykjavik babban birnin kasar Iceland.

Reykjavik nan ne inda aka gudanar da taron koli na shekara ta 1986- lokacin da na dab da kawo karshen yakin cacar baka tsakanin shugaba Ronald Reagan da Mikhail Gorbachev, shugabannin Amurka da na Tarayyar Soviet a wancan lokacin.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An san Mr Trump da wallafa kalamai masu karfi a shafinsa na Twitter

Mr Brennan ya ce surutai da rubuce-rubuce a shafin Twitter, ba shine mafita ba ga Mr Trump wanda zai karbi mulki a ranar Jumma'a mai zuwa.

Ya kuma ce " Wannnan ya wuce batun Trump kawai. Batu ne na Amurka gaba daya.''