Taron Paris: An gargadi Isra'ila da Falasdinawa

Jami'an manyan kasashen duniya da suka halarci taron

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Kasar Faransa dai ce ta jagoranci taron na ranar Lahadi.

Wakilan kasashen da suka halarci taro kan zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa a birnin Paris sun gargadi bangarorin biyu da su daina yin gaban kansa wajen daukar kowane irin mataki.

A cikin wata sanarwar bayan taron, wakilan sun kuma jaddada goyon bayansu ga kafa kasar Falasdinu a zaman hanyar magance rikicin.

Falasdinawa dai sun yi na'am da yin taron yayin da Isra'ila ta kira shi taron da aka riga aka tsara yadda sakamakonsa zai kasance.

Ba a dai bai wa kowane bangare damar halartar taron wanda kasashen duniya 70 suka halarta ba, amma an gayyato kowanne don ya ji matsayar da aka cimma.

Taron dai ya zo ne a daidai lokacin da zaman tankiya ke kara kamari a yankin Gabas ta Tsakiya kuma ake fargabar shirin da Donald Trump ke yi na sauya wa ofishin jakadancin Amurka a Isra'ila mazauni daga Tel Aviv zuwa birnin Kudus zai kara dagula al'amarin.