Zakzaky: An bukaci Nigeria ta mutunta dokokinta

Masu zanga-zangar neman sakin El-zakzaky
Bayanan hoto,

Haka ma kotun ta ce a biya Zakzaky da Zinatu diyar Naira miliyan 50 kowanne.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce ya kamata hukumomin Nigeria su yi aiki da umarnin da wata babbar kotu ta bayar su gaggauta sakin jagoran kungiyar IMN Ibrahim El-zakzaky da mai dakinsa da suke tsare da su.

Fiye da shekara daya kenan da aka tsare Sheikh Zakzaky da matarsa Zennatu Ibrahim ba tare da an tuhumesu a kotu ba, bayan wani rikici tsakanin sojan Nigeria da magoya bayan malamin wanda ya yi sanadin mutuwar 'yan kungiyarsa ta IMN 347.

Hukumomin tsaron kasar dai sun ce ana tsare da shi don ba shi kariya, amma malamin ya kalubalanci hakan a kotu kuma ya yi nasara a shari'ar.

A ranar 2 ga watan Disamban da ya gabata kotun ta yanke hukuncin cewa tsarewar da ake yi masa ta saba wa doka kuma ta umarci a sake shi cikin kwanakki 45.

''A yau ne wannan wa'adin na kwanakki 45 ke karewa. Idan gwamnati ta yi biris da umarnin kotun kasarta, wannan zai zama tsabagen rashin mutunta doka - wanda abu ne mai hadari,'' in ji Makmid Kamara daraktan kungiyar a kasar.