'Yan Gambia suna tserewa saboda fargaba

Gambia
Bayanan hoto,

Yahya Jammeh ya shigar da ƙorafi kotun ƙoli a kan zaɓen

Al'ummar Gambia da ke fargabar ɓarkewar rikici suna tserewa daga ƙasar, yayin da ranar miƙa mulki a hukumance take ƙarasowa.

An ga daruruwan mutane cunkushe suna ƙoƙarin hawa jirgin ruwa don tserewa, ta wani yanki da ke haɗa ƙasar da Senegal.

Akasarinsu mata ne da ke riƙe da ƙananan yara, wata uwa ta faɗa wa BBC cewa "Mu hudu ne. Barin ƙasar za mu yi saboda rashin tabbas."

Sai dai wata mata kuma da aka gan ta a kan hanya ta ce ita ba za ta bar Gambia ba, amma dai za ta gudu daga Banjul, babban birnin ƙasar.

Ta ce "Zan tafi Nyomi saboda ina tsoro a nan. Zan tafi can wajen dangina. Ban san mai zai faru ba a Banjul, idan hankali ya kwanta. Zan dawo"

Mutanen da ke tserewa na tafiya zuwa Senegal da Guinea da Saliyo ne.