Murar tsuntsaye ta barke karon farko a Uganda

Agwagwa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Hukumomin suna wayar da kan mutane domin su kula kada cutar ta yadu zuwa ga mutane

Gwamnatin Uganda ta tabbatar da barkewar cutar murar tsuntsaye a wasu yankunan da ke kusa da tafkin Victoria.

An gano cutar ce a jikin tsuntsayen da ke gudun hijira zuwa kasar, da kuma agwagi da kaji na gida.

Hukumomi suna wayar da kan al'ummomin da ke yankunan a kokarinsu ganin cutar ba ta yadu zuwa ga mutane ba.

A farkon sabuwar shekarar nan ce aka samu rahoton mutuwar wasu tsuntsaye sakamakon cutar murar tsuntsayen.

Mutanen gari sun ce sun ga gawarwakin tsuntsayen da ke gudun hijira zuwa arewacin kasar a lokacin sanyi.

Gwaje gwajen da aka yi daga baya sun tabbatar cewa sun mutu ne sakamakon cutar. Haka ma gwajin da aka yi a kan wasu agwagi da kaji a wata gunduma ya gano tsuntsayen na dauke da cutar.

An aike da kungiyoyin agajin gaggawa don tattaro gawarwakin tsuntsayen.

Wannan ne dai karon farko da aka samu barkewar cutar murar tsuntsaye a kasar ta Uganda inda hukumomi suka kware wajen bayar da agajin gaggawa bayan da suka shawo kan annobar Ebola.