Uwa ta tunkuɗa 'ya'yanta ruwa a Australia

Guode

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Guode a lokacin da aka yi jana'izar yaran da suka mutu

Wata uwa ta kashe yaranta uku, bayan ta jefa su a wani tafki da ke kudancin Australia daga mota.

Guode ta amsa laifin kashe 'ya'yanta da laifin aikata kisan gilla biyu da kuma yunkurin kisan kai a gaban kotun koli ta garin Victoria

Matar wadda ta amsa haka ta bakin mai fassara ta isa Australia ne daga Sudan a shekarar 2008.

An tuhumi Akon Guode mai shekara 37 da kashe jaririnta Bol mai shekara daya da kuma 'yan biyunta Hanger da Madit masu shekara 4 a kudu maso yammacin Melbourne a shekarar 2015.

Alual mai shekara 6 na cikin motar amma kuma Allah ya tserar da ita.

A lokacin da ake sauraron karar, Joseph Manyang mahaifin yaran ya sanar cewa Guode ta ce tana jin kanta yana juyawa kafin faruwar al'amarin.

Ya bayyana matarsa a matsayin "uwa mai son 'ya'yanta" wadda ba za ta cutar da su da gangan ba.

Sai dai wani ƙwaƙƙwaran shaida ya fada wa 'yan sanda a wata sanarwa da suka fitar cewa ta yi ikirarin kashe yaranta a ranar da iftila'in ya faru.