Trump ya ce Birtaniya na kokari bayan barin Tarayyar Turai

Donald Trump

Asalin hoton, Times

Bayanan hoto,

Donald Trump ya yi alkawarin cimma yarjejeniyar bunƙasa kasuwanci tsakanin Birtaniya da Amurka

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya ce Burtaniya ta yi kokari da ta zaɓi barin Tarayyar Turai.

A zantawarsa ta farko a Birtaniya da tsohon sakataren shari'ah, Michael Gove - Donald Trump ya ce a ganinsa Birtaniya "ta yi farar dabara, wajen barin Tarayyar Turai.".

Mr Trump ya yi alkawarin cewa nan ba da dadewa ba za su rattaba hannu a kan yarjejeniyar bunkasa kasuwanci tsakanin Amurka da Birtaniya, rantsar da shi ranar Juma'a mai zuwa.

Ya kuma soki lamirin Nato wadda ya kira "tsohuwar yayi" da kuma manufofin shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel a kan harkokin shigi da ficen kasar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ana shirye-shirye a Washington don rantsar da shugaban Amurka ranar juma'a

Mr Trump ya ce Mrs Merkel ta yi "kuskure" da ta amince da shigar dumbin 'yan gudun hijira har fiye da miliyan ɗaya zuwa kasar.

Ya kuma ce zai "fara amincewa da shugaban Rasha Vladimir Putin da kuma Mrs Merkel" da zarar ya kama aiki don ganin iya gudun ruwansu.

A watan Nuwamban bara, fadar Downing Street ta ce firaminista, Theresa May da Mr Trump sun tattauna ta wayar tarho kan muhimmancin samun ƙarin kasashe da za su riƙa keɓe kashi biyu cikin 100 na kuɗin shigarsu ga harkokin tsaro, bayan Trump ya ci zaɓe.