Ungozomomi a Sweden za su koya wa mata yadda za su haihu a cikin mota.

Kafafuwan wani jariri sabuwar haihuwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ungozomomin sun ce za su rika taimaka wa mata masu juna biyu yadda idan ta kama za su iya haihuwar jariransu a cikin mota

An yi wa mata masu juna biyu a garin Solleftea na kasar Sweden tayin karbar horo kan yadda za su iya haihuwar jariransu a cikin mota, yayin da ake shirin rufe sashen haihuwa na yankin.

Wasu ungozomomi biyu ne a asibitin na Solleftea suka bullo da shawarar don taimakawa matan , da mazajensu samun natsuwa a lokacin da suke kan doguwar tafiya zuwa asibiti, kamar yadda jaridar The Local ta bayar da rahoto.

Stina Naslund, wacce za ta jagoranci koyarwar, ta ce ta san mutane da dama na fargabar yin tafiya mai nisa cikin yankunan karkara, musamman lokacin yanayin duhun hunturu.

''Komai na iya faruwa idan haihuwa ta zo''

Ms Naslund ta shaidawa jaridar ''The Local'' cewa tana son ta ankarar da mutane abinda ka iya faruwa. '' Hadarin mota, ko lalacewar mota, za ka iya kaucewa hanya. Dole ka zama cikin shiri, ko da kuwa hakan bai saba faruwa ba,'' ta ce.

Horon zai hada da yadda za a yi idan haihuwar ta zo a gaggauce.

Matakin rufe sashen masu haihuwa a Solleftea, mai yawan jama'a kusan 9,000, wani bangare ne na shirin tsuke bakin aljihu da aka yi kudiri cikin watan Oktoba, in ji jaridar Expressen.

Mia Ahlberg, shugabar kungiyar ungozomomi ta kasar Sweden ta goyi bayan batun horar da mata masu juna biyun, amma kuma ta ce '' abin bakin ciki ne'' cewa ana bukatar hakan ne kawai saboda za a rufe dakunan haihuwa na asibitin yankin.