'Birtaniya za ta fice daga Turai kacokan'

Firai Ministar Birtaniya Theresa May

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Theresa May na son Birtaniya ta yi watsi kacokan da wasu yarjeniyoyi da Tarayyar Turai

Firai ministar Birtaniya, Theresa May, ta sanya wasu batutuwa guda 12 da ta ce su ne mafi mahimmanci ga fitar kasar tata daga Tarayyar Turai.

Misis May ta kuma kara da cewa tana son Birtaniya ta fice daga tarayyar dungurungum ba wai rabi da rabi ba.

Nan gaba kadan ne dai a ranar Talatar nan ake sa ran Firai ministar za ta yi wani jawabi ga 'yan kasar kan jadawalin da ta fitar wajen ficewa daga Tarayyar Turai.

Ana dai sa ran Birtaniya za ta fara shirin ficewa daga Tarayyar ta Turai ne, kafin karshen watan Maris.