Brazil za ta gina gidajen yari 30 don rage cunkoson 'yan sarka

Michel Temer shugaban kasar Brazil

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Michel Temer na ganin ta haka ne za a rage cunkoso a gidajen sarka na Brazil

Shugaban Brazil, Michel Timere, ya ce za a gina sabbin gidajen kaso har guda 30 a fadin kasar, a tsawon shekara guda, da nufin rage cunkosan da gidajen yarin kasar ke fama da shi.

Biyar daga ciki za su zama na masu manyan laifuka wadanda a ciki ne za a sa 'yan daba wadanda suka jefa gidajen yarin cikin halin da suke ciki a yanzu, na hargitsi da tayar da kayar baya a arewacin kasar.

Akalla dai an kashe mutane 140 sakamakon arangama tsakanin kungiyoyin 'yan daba biyu wadanda ba sa ga-maciji da juna, a gidajen na-kaso a wannan shekara.