Gambia: Kare ya kashe dan Adama Barrow

Adama Barrow

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Adama Barrow bai halarci jana'izar dan nasa ba, saboda ya gudu zuwa Senegal

Kare ya kashe dan sabon zababben shugaban kasar Gambia Adama Barrow, sakamakon cizonsa da ya yi.

Rahotanni sun ce Habibu Barrow dan shekara 8, ya rasu ne a kan hanyar kai shi asibiti ranar Lahadi a garin Manjai kusa da babban birnin kasar, Banjul.

Adama Barrow bai samu damar halartar jana'izar dan nasa ba saboda ya kaurace wa kasar zuwa Senegal saboda kare lafiyarsa.

Barrow ne ya yi nasara a zaben kasar na watan Nuwamba, amma shugaba Yahya Jammeh ya ki amincewa da sakamakon bayan da ya yarda ya sha kaye.

Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, Ecowas, ta bukaci Adama Barrow ya zauna a Senegal har zuwa ranar Alhamis, ranar da ya kamata a rantsar da shi.