China na bincike kan sinadaran ɗanɗanon girki 'na jabu'

Amfani da sinadaran dandano ya zama jiki a Asiya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Amfani da sinadaran dandano ya zama jiki a Asiya

Hukumomi a kasar China na biciken kusan kamfanoni 50 saboda zargin da ake yi musu na amfani da sinadaran ɗanɗanon girkin da ba a yi wa rijista ba.

An dauki matakin ne bayan jaridar Beijing News ta bankado yadda kamfanonin ke amfani da sinadaran kusa da birnin Tianjin.

Kamfanonin na yin amfani da sinadaran da suka hada da gishirin da ake amfani da shi a ayyukan masana'antu .

Sun sanya wa sinadaran a jikin Maggi, Knorr, da Nestle.

Sinadaran, wadanda suka hada da kayan kanshi da ruwan nama, na cikin abubuwan da ake amfani da su wajen girke-girke a china da ma sauran yankunan nahiyar Asiya.

A 'yan shekarun bayan bayan nan, ana samun badakala kan yadda ake amfani da kayan abinci a China, inda a shekarar 2008 aka gano wata gurbatacciyar madarar jarirai wacce ta sanya wa jarirai kusan 300,000 cutuka.

Abinci maras tsafta

Wata sanarwa da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta China ta fitar ranar Litinin ta ce ta akie da jami'anta zuwa Tianjin domin yin bincike kan lamarin.

Ita dai jaridar Beijing News ta ce kamfanonin yin sinadaran sanya dandanon abinci na jabu na karuwa a yankin ba tare da an sanya musu ido ba.

Kamfanoni kusan 50 na yin sinadaran dandadon abinci na jabu, inda suke samun kusan $14.5m a duk shekara.

A makon jiya ne 'yan jarida da 'yan sandan da suka yi bad-da-kama suka je wasu masana'antu domin ganin abubuwan da suke yi.