Tsohon kocin Man Utd Van Gaal ya yi ritaya

Van Gaal ya dage kofin FA a watan Mayu na 2016 - kuma awowi kadan bayan hakan aka kore shi daya United

Asalin hoton, Empics

Bayanan hoto,

Van Gaal ya dage kofin FA a watan Mayu na 2016 - kuma awowi kadan bayan hakan aka kore shi daya United

Tsohon kocin Manchester United da Netherlands Louis van Gaal ya ce ya yi ritaya bayan ya kwashe fiye da shekara 26 yana aiki.

Van Gaal, mai shekara 65, ba shi da aiki tun bayan korar sa da United ta yi awowi kadan bayan sun ci kofin FA a watan Mayu na shekarar 2016.

Ya shaida wa jaridar De Telegraaf ta kasar Netherlands cewa, "Da na yi zaton zan dan huta ne, sai kuma na ga ya kamata na tafi hutu sosai kuma ina ganin ba zan dawo horas da 'yan wasa ba."

Van Gaal ya taba yin kocin Ajax, Barcelona, Bayern Munich da kuma AZ.

Ya bayar da sanarwar yin ritayar tasa ne ranar Litinin bayan ya karbi wata lambar yabo daga wurin gwamnatin aNetherlands saboda gudunmawar da ya bayar a fagen tamaula.

Van Gaal ya ce ya dauki matakin ne domin ya kula da iyalinsa, sai dai jaridar De Telegraaf ta ce mutuwar sirikinsa na cikin abubuwan da suka sanya shi yin ritaya.