An kama Paston da ya yi hasashen mutuwar Robert Mugabe

Patrick Mugadza, the pastor who predicted Mugabe would die in October

Asalin hoton, Patrick Mugadza

Bayanan hoto,

Wannan ba shi ne karon farko da aka kama Patrick Mugadza ba

An kama wani Pasto a kasar Zimbawea wanda ya yi hasashen cewa shugaban kasar Robert Mugabe ya kusa mutuwa.

A makon jiya ne Patrick Mugadza ya bayar da sanarwar cewa shugaban kasar mai shekara 92 a duniya zai mutu ranar 17 ga watan Oktoba mai zuwa.

Lauyansa, Gift Mtisi, ya shaida wa BBC cewa paston ya yi hasashen ne bisa "sakonnin da ya samu daga wurin ubangiji. Dole 'yan sanda su kawo hujjar da za ta nuna cewa sakon ubangijin ba gaskiya ba ne".

Mr Mugabe ya yi raha kan hasashen mutuwar da aka rika yi a kansa a kwanakin baya, yana mai cewa zai rika mutuwa yana tashi.

Mr Mtisi ya ce da farko an tuhumi paston da laifin rashin biyayya ga ayyukan shugaban kasa, amma daga baya aka tuhume shi da aikata laifuka.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mr Mugabe, mai shekara 92, ya ce idan ya mutu zai tashi