Tsoron barkewar rikici ya sa 'yan yawon bude ido na tsere wa daga Gambia

Beach in Gambia

Asalin hoton, PA

Dubban 'yan kasar Birtaniyan da kamfanin yawon bude ido na Thomas Cook ke mu'amala da su na fice wa daga Gambia suna komawa kasarsu bayan ma'aikatar kasashen waje ta ba su shawarar yin hakan.

Kamfanin ya ce zai yi jigilar 'yan yawon bude ido 985 daga wuraren da suke shakatawa na Gambia nan da kwana biyu masu zuwa.

Ya kara da cewa zai aike da jirgin da zai kwashe mutum 2,500 daga kasar ta Gambia cikin gaggawa.

Wata sanarwa da Thomas Cook ya fitar ta ce: "Za mu aike da karin jirage zuwa filin jirgin saman Banjul nan da kwana biyu domin su kwashe masu mu'amala da mu 'yan kasar Birtaniya 985, wadanda a yanzu haka suke can suna hutu domin komawa da su gida. Za mu karo jirage hudu ranar Laraba 18 ga watan Janairu".

Ma'aikatar harkokin kasashen wajen ta bayar da shawarar cewa kada wani dan kasar ya je Gambia saboda yiwuwar barkewar rikici.

Gwamnatin Gambia ta sanya dokar ta-baci ta kwana 90.

Shugaba Yahya Jammeh ya ce ba zai sauka daga mulki ba saboda zargin da ya yi cewa an tafka kura-kurai a zaben da aka yi a watan Disamba.

Sai dai Adama Barrow, mutumin da ya lashe zaben, ya ce za a rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar ranar Juma'a kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya bukaci a yi.

Tuni dai Najeriya, wacce shugabanta Muhammadu Buhari ke jagorantar gano bakin-zaren rikicin na Gambia, ta aike da jirgin ruwan yaki kusa da kasar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Yahya Jammeh ya shafe shekara 22 a kan mulki