Za ka so a keɓe wurin zaman mata a jirgin sama?

Wasu mata a cikin jrigi
Bayanan hoto,

Kamfanin jirigin saman Indiya ya bullo da sabon tsarin ne bayan wasu mata sunyi korafin ana shashafasu a cikin jrigin

Kamfanin jirgin saman Indiya ya kebe kujeru shidan farko a jiragensa samfurin Airbus A320 ga mata bayan wasu sun yi korafin ana shassshafa su.

Za a aiwatar da wannan mataki ne a inda kujerun shida na farko a ajin masu matsakaicin kudi.

Manajan jirgin ya shaida wa jaridar The Hindu cewa suna so su kara tabbatar da kare lafiyar matan.

Meenakshi Malik ya ce "A matsayin mu na ma'aikata masu kula da jirgin saman kasar, hakkinmu ne mu kara walwalar fasinjojinmu mata da ke shiga jiragenmu.

Jirgin zai rika daukar mutum biyu wadanda za su rika shawo kan fasinjojin da ke haddasa irin wannan fitinar kuma ba za a iya hana su ba.

Daga karshen wannan makon, jirgin Indiya kirar A320 zai bai wa mata damar amfani da kujeru shidan farko da ke bangaren da ake biyan matsakaicin kudi.

Akwai yiwuwar za a samar da irin wadannan kujeru a wasu jiragen kasar a watanni masu zuwa.

Fasinjan da ba shi da abokin tafiya yana da damar yin amfani da kujerar a lokacin da zai shiga jirgi.

Sai dai ba duka mutanen da ke amfani da jirgin ne suka yi maraba da sabon tsarin ba.

Jitendra Bhargava shi ne tsohon shugaban kamfanin jirigin Indiyan kuma ya shaida wa jaridar The Hindu cewar "A iya sani na, ba a taba yin haka a ko ina a duniya ba. Jirigin sama ba hadari ba ne ga fasinjoji mata."