Jiragen yakin Nigeria sun jefa bam kan fararen hula 'bisa kuskure'

Sojin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sojin Najeriya na fafatawa da Boko Haram a Arewa maso Gabashin kasar

Mutane da dama ne ake fargabar sun rasa rayukansu bayan da jiragen yakin sojin Najeriya suka jefa bama-bamai bisa kuskure kan fararen hula a kauyen Raan a jihar Borno.

Rundunar sojin ta ce cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, wanda ya faru a karamar hukumar Kale-balge, sun hada da jami'an lafiya na MSF da kungiyar agaji ta Red Cross.

Shugaban rundudar yaki da Boko Haram Manjo Janar Lucky Irabor ya shaida wa manema labarai cewa an samu mutuwa da raunuka a harin.

Ya kara da cewa har da sojoji a cikin wadanda suka jikkata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa kan lamarin.

Mai magana da yawun rundunar tsaro ta Najeriya Janar Rabe Abubakar ya shaida wa BBC cewa sun kadu kan wannan kuskure da ya faru.

Agajin gaggawa

Ya ce lamarin ya faru ne bayan sun samu labarin cewa mayakan Boko Haram sun taru a wani waje da shirin kai hari.

''Amma a bisa tsautsayi sai ya fada wannan kauye. Ba da niyya mu kai hakan ba, kuma hakan dama kan faru a yankunan da ake yaki,'' in ji Janar Rabe.

Jami'in ya jajanta kan lamarin inda kuma ya ce har yanzu ba a san adadin mutanen da suka mutu ba, ''amma muna ci gaba da bincike,'' in ji shi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dakarun Najeriya na amfani da jiragen yaki wajen farautar 'yan Boko Haram

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya umarci da a bayar da agajin gaggawa ga dukkan wadanda lamarin ya rutsa da su.

Mista Shettima ya nemi asibitocin gwamnati da motocin daukar marasa lafiya da su zauna cikin shirin ko-ta-kwana domin agazawa wadanda harin ya shafa.

Wata sanarwa da ofishin gwamnan ya fitar ta ambato shi yana cewa kawo yanzu babu cikakken adadin wadanda lamarin ya rutsa da su.