Shin wanene farfesan da BH ta kashe a Maiduguri?

Marigayi Farfesa Mani na Jami'ar Maiduguri

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Farfesa Aliyu Usman Mani ya mutu ya bar mace daya da 'ya'ya biyu

A ranar Litinin ne kungiyar Boko Haram ta kai wasu hare-haren kunar bakin wake jami'ar Maiduguri a karon farko.

Hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutum hudu da suka hada da Farfesa Aliyu Mani, wanda malami ne a jami'ar.

Takaitaccen tarihin Farfesa Mani

Farfesan wanda dan asalin jihar Katsina ne an haife shi a watan Afrilun 1957 a birnin Katsina.

Ya fara karatu a makarantar firamare a Kayalwa a jihar Katsina daga shekara ta (1964-1970) , ya yi kuma karatun sakandare a Kwalejin gwamnati ta Kaduna daga (1971-1975).

Daga nan ya zarce makarantar share fagen shiga jami'a SBS dake jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria ABU.

Bayan kammala karatunsa ya samu shiga tsangayar nazarin kula da lafiyar dabbobi a jami'ar ta ABU Zaria, ya kuma samu takardar shaidar digirin digirgir a fannin kula da lafiyar dabbobi DVM a shekarar 1981.

Ya yi aikin yi wa kasa hidima NYSC da makarantar koyon ayyukan gona da ke Asaba a jihar Bendel.

Ya yi takaitaccen aiki a hukumar raya tafkin Niger a garin Ilori jihar Kwara, kafin ya koma jami'ar Maiduguri a matsayin mataimakin malamin jami'a a tsangayar nazarin kula da lafiyar dabbobi a cikin watan Oktabar shekara ta 1982.

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Farfesa Aliyu Usman Mani ya koma jami'ar Maiduguri a watan Oktobar shekarar 1982

Daga bisani ya halarci cibiyar bincike mai zurfi a fannin nazarin kula da lafiyar dabbobi a jami'ar Edinburgh da ke kasar Birtaniya, inda ya samu takardar shaidar kammala digiri na biyu da kuma digirin digirgir.

Ya sake komawa jami'ar Maiduguri a shekara ta 1994.

Farfesa Mani ya zama mamba a kungiyar likitocin fida na dabbobi a shekarar 2010. Ya kuma taba zama daraktan Asibitin Koyarwa na kula da lafiyar dabbobi na jami'ar Maiduguri a shekarar 1997 zuwa 2000.

Ya kuma zama shugaban tsangayar nazarin kula da lafiyar dabbobi tsakanin 2005-2010, kana mukaddashin daraktan tsangayar a 2008-2010.

Kafin rasuwarsa Farfesa Aliyu Mani shi ne daratkan asibitin koyarwa a fannin kula da dabbobi na jami'ar Maiduguri.

Ya kuma rike mukamai da dama a ciki da wajen jami'ar.

Ya mutu ya bar mace daya da 'ya'ya biyu.