Nigeria 'ta tura jirgin ruwan yakinta zuwa Gambia'

Njaeriya Gambia

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Najeriya ce ta fi kowacce kasa karfin soji a yankin

Najeriya ta tura jirin ruwan yaki Gambia, a wani mataki na shirin kai farmakin soji idan Shugaba Yahya Jammeh ya ki mika mulki bayan cikar wa'adinsa ranar Alhamis.

Wata majiya a rundunar sojin kasar ta shaida wa BBC cewa, bayan tashinsa daga birnin Lagos, yanzu haka jirgin ruwan mai suna NNS Unity na tunkarar gabar tekun kasar Ghana.

A cikin karshen makon nan ne shugabannin kasashen Afirka ta yamma suka gana, kan shirin tura dakarun shirin ko-ta-kwana na kungiyar ECOWAS zuwa Gambia.

Hakan ya biyo bayan ziyarar da shugabannin suka kai birnin Banjul, don jan hankalin Shugaba Jammeh ya mika mulki ga Adama Barrow, wanda ya kayar da shi a zaben da aka gudanar cikin watan Disamba.

Kasar Senegal wacce ke jagorantar ayyukan sojin, ta shirya nata sojojin gabanin wa'adin ranar Alhamis na saukar Shugaba Jammeh daga mulki.

A shekarun baya-bayan nan Mista Jammeh ya yi ta yiwa na hannun daman shi karin girma, da suka hada da hafsan sojin kasar Ousman Badjie - a ko wacce shekara su kan samu karin matsayin da ya wuce cancantarsu.

Hakan dai ya kara kaskantar da yanayin tsarin aikin sojin kasar.

Kungiyar ECOWAS ta jajirce a kan cewa amfani da karfin soji ita ce mafitar da za ta kawo karshen dambarwar siyasa a kasar ta Gambia idan Jammeh ya ki sauka.