Gambia: Jammeh ya ayyana dokar ta-baci ta kwanaki 90

Gambia Jammeh

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Yahya Jammeh ya yi watsi da sakamakon zaben

Shugaban Gambia mai barin gado Yahya Jammeh ya ayyana dokar ta-baci ta kwanaki 90, kwana guda kafin cikar wa'adin mulkinsa kamar yadda gidan talabijin na kasar ya sanar.

Shugabannin kasashen Afirka ta yamma sun yi ta kokarin shawo kan shi ya mika mulki ga Adama Barrow, wanda ya kayar da shi a zaben watan Disambar da ya gabata.

Matakin na zuwa ne jim kadan bayan da Najeriya ta tura jirgin ruwan yakinta don kara matsin lamba kan Mista Jammeh.

Kungiyar ECOWAS ta shirya dakarunta, kuma tana kan bakanta cewa amfani da karfin soja ne mafitar da za ta kawo karshen dambarwar siyasar kasar.

Babu wani tabbaci kan irin dokar ta-bacin, saboda ba a bayar da wasu cikakkun bayanai a cikin sanarwar ba.

A ranar Alhamis ne ake sa ran rantsar da Adama Barrow a matsayin sabon shugaban kasar.