Jiragen yakin Nigeria sun kashe 'fararen hula 52' bisa kuskure

Matukin jirgin dai ya yi tunanin mutanen 'yan Boko Haram ne

Asalin hoton, AFP/MSF

Bayanan hoto,

Mutane fiye da 120 ne dai ake tunanin sun jikkata

Rahotanni na cewa wani jirgin yakin sojin saman Najeriya, ya hallaka mutane 52 sakamakon ruwan bama-bamai da ya yi a kan sansanin 'yan gudun hijra a kauyen Rann na jihar Borno, bisa zargin cewa 'yan Boko Haram ne .

Ma'aikatan agaji na cikin wadanda suka samu raunuka - kungiyar bada agaji ta Red Cross ta tabbatar da mutuwar shida daga cikin ma'aikatanta.

Kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta duniya, MSF ta ce tana kula da wadanda suka jikkata guda 200.

Harin ya faru ne a kauyen Rann da ke kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru, inda sojoji ke fafatawa da mayakan Boko Haram.

Rundunar sojin sama ta Najeriya dai ta ce al'amarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 50 tare da jikkata 100.

Wani kwamanda a rundunar sojin Najeriya Manjo Janar Lucky Irabor ya ce matukin jirgin yakin ya kai hari kan mutanen ne a bisa kuskuren cewa 'yan Boko Haram ne.

Ya ce an bashi umarni ne a bisa bayanan sirri game da wuraren taruwar mayakan Boko Haram.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da sakon nuna takaici da kuma jaje, game da asarar rayukan da aka yi, ya kuma yi kira da a kwantar da hankali.

Asalin hoton, AFP/MSF

Bayanan hoto,

Irin hotunan da kungiyar Likitoci ta kasa da kasa ta MSF ta fitar kenan

Kakakin fadar shugaban kasar, ya ce gwamnati za ta tallafawa gwamnatin jihar Borno game da wannan abin bakin ciki da ya faru.

Kakakin kungiyar MSF Etienne l'Hermitte ya yi kira ga mahukuntan Najeriya da su taimaka wajen kwashe mutanen da suka samu raunuka ta sama da ta kasa.

"Jami'an kiwon lafiyarmu a kasashen Kamaru da Chadi a shirye suke su duba wadanda suka jikkata", in ji shi.

MSF ta ce akasarin wadanda harin ya rutsa da su mutanen da suka gudu daga matsugunansu ne a yankunan da 'yan Boko Haram ke kai hare-hare.

Rahotanni sun ce lamarin dai ya rutsa da jami'an tsaro da dama, inda wasu suka mutu yayin da wasu kuma suka samu raunuka.

Rundunar sojin ta ce tana amfani da jirage masu saukar ungulu domin kwashe wadanda suka jikkata.

Asalin hoton, AFP/MSF

Bayanan hoto,

Wannan dai shi ne karon farko da irin haka ta faru a Najeriya