Wikileaks: Obama ya yi wa Chelsea Manning afuwa

Chelsea Manning

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Ainahi Chelsea Manning namiji ne ya sauya halittarsa ya koma mace

Shugaba Barrack Obama ya zaftare hukuncin zaman gidan yari na shekara 35 da aka yanke wa wata mata sojar kasar, saboda bayar da bayanan sirrin kasar da ta yi, wanda ya fi kowanne muni a Amurka.

Sakamakon afuwar Shugaban yanzu Manning Chelsea wadda aka yanke wa hukuncin a 2013, za ta samu 'yancinta a watan Mayu, maimakon shekara ta 2045.

Kakakin majalisar wakilan kasar Paul Ryan, ya ce hukuncin da Shugaba Obama ya dauka abu ne mai sosa rai sannan kuma hakan na nufin duk wanda ya bankada asirin tsaron kasa to ba za a hukunta shi ba.

Shafin kwarmata bayanai na Wikileaks wanda Manning ta ba wa miliyoyin bayanan sirri, ya bayyana sakin nata da cewa nasara ce, yayin da masu suka ke cewa babban kuskure ne.

Matar mai shekara 29 an haife ta ne namiji da sunan Bradley Manning, kafin daga bisani ta sauya ta koma mace.