Zargin lalata: An kai karar Donald Trump kotu

Summer Zervos na daya daga cikin tarin matan da suka zargi Mista Trump ta cin zarafinsu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Summer Zervos ta ce ba ta da zabi illa ta kai karar Mista Trump domin ta dawo da kimarta

Wata mata Summer Zervos da ta zargi shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump da sumbatarta tare da taba mata jiki, ta kai kararsa kotu bisa keta mata mutunci saboda karyata zargin nata.

Makonni kafin nasarar da ya samu a zaben shugaban Amurka, Donald Trump ya fuskanci jerin zarge-zargen lalata da mata da yawa ciki har da Summer Zervos.

Tun a lokacin Mista Trump ya yi ta karyata zarge-zargen.

Matar dai tana son kotu ta bi mata kadin mutumcinta da ta ce Donald Trump ya zubar mata, saboda ya ce zargin da ta yi masa ba shi da tushe.

Ms Zervos ta kasance a lokacin daya daga cikin masu shiga shirin talabijin na Mista Trump, wanda ake kira 'The Apprentice'.