Masar ta sanya tsohon dan kwallo Mohamed Aboutrika cikin 'yan ta'adda

Mohamed Aboutrika of Al-Ahly SC at the FIFA Club World Cup Quarter Final match against Guangzhou Evergrande FC in Morocco, 14 December 2013

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mohamed Aboutrika ya boyi bayan Mohamed Morsi a shekarar 2012

Masar ta saka tsohon fitaccen dan kwallon kafar kasar Mohamed Aboutrika cikin jerin sunayen 'yan ta'adda saboda mu'amalar da yake yi da kungiyar 'Yan Uwa Musulmi wadda aka haramta, a cewar lauyansa.

Ana zargin Mr Aboutrika da tallafawa kungiyar ta 'Yan Uwa Musulmi da kudi, matakin da hukumomin Masar ke yi wa kallo a matsayin aikin ta'addanci.

A shekarar 2012, ya goyi bayan dan takarar shugabancin kasar dan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi, Mohamed Morsi, wanda ya lashe zaben.

Matakin da gwarzon dan kwallon kafar BBC na shekarar 2008 ya dauka ya sanya wasu masu goyon bayansa sun kaurace masa.

Duk mutumin da aka sanya a jerin 'yan ta'addar zai iya fuskantar hukuncin hana shi fita daga kasar da kwace fasfo dinsa da kuma hana shi taba kaddarorinsa.

Lauyan Mr Aboutrika, Mohamed Osman, ya ce matakin da hukumomin suka dauka ya "sabawa dokokin kasar", yana mai cewa ba a tuhumi mutumin da yake wakilta da laifin komai ba.

Ya kara da cewa za su daukaka kara a kan batun.

Mr Aboutrika ya musanta zargin da ake yi masa.