Kun san manyan na hannun-daman Trump?

Asalin hoton, Getty Images
Trump ya zargi matar Obama da cewa bata iy komai ba sai yakin neman zabe
A matsayinsa na sabon shugaban Amurka, Donald Trump zai karɓi iko da fadar White House, mun yi nazari kan iyali da abokan hulɗar da za su kasance cikin jami'ansa da kuma ka iya samun muhimman muƙamai a shugabancinsa.
'YAN SIYASA
Sabon mataimakin shugaban ƙasa Mike Pence
Gwamnan jihar Indiana, ɗan shekara 57, shi ne ke jagorantar ayarin masu yanke shawara kan muhimman naɗe-naɗen da za a yi a sabuwar gwamnati.
Yana da tagomashi a tsakanin masu ra'ayin 'yan mazan jiya kuma yana taƙama da ɗumbin gogewar da yake da ita a Washington.
Mike Pence da 'yan'uwansa biyar masu bin Roman Katolika ne da suka taso a Columbus, ta jihar Indiana, kuma ya samu zimma daga fitattun masu sassaucin ra'ayi irinsu John F Kennedy da Martin Luther King Jr.
Ya shahara da gagarumar adawarsa kan zubar da ciki. Duk da haka ya ce zai yi aiki da hukuncin da Kotun Koli ta kifar a 1973, da ya haramta wa gwamnatin Amurka hana zubar da ciki.
Ya riƙe shugabancin 'yan majalisa na jam'iyyar Republican, muƙami na uku mafi girma a shugabancin Republican.
Asalin hoton, Reuters
Rex Tillerson - Sakataren wajen Amurka
Rex Tillerson, shi ne mutumin da Trump ya bayyana a matsayin "wani ƙusa da ake ji da shi a duniya", kuma ya jagoranci kamfanin harkokin man fetur mai daraja da ɗumbin hada-hada.
An san kusancin shugaban na Exxon Mobil da alaƙarsa ta ƙut-da-ƙut da Vladimir Putin; a shekara ta 2013, Rasha ta bai wa ɗan Texas ɗin wata lambar yabo ta Order of Friendship award.
'Yan jam'iyyar Republican da takwarorinsu na Dimokrat sun tuhumi alaƙar Rex Tillerson da shugaban Rasha.
Ɗan shekara 64, ya shafe tsawon shekarunsa na aiki, sama da shekara 40, a Exxon Mobil.
A tsawon shekara goman da ta wuce ya samu fiye da Dala miliyan 240 a matsayinsa na babban jami'in Exxon, yanzu kuma zai riƙa karɓar abin da bai fi Dala 203,700 a shekara ba.
Steven Mnuchin - Sakataren Baitul-mali
Donald Trump da kansa ya yi ƙila-wa-ƙala kan tunanin bayar da sunan Mnuchin don jagorantar harkokin kuɗin Amurka kafin daga bisa a bayyana shi a matsayin mutumin da za a naɗa.
Yayin sanar da shawarar, Trump ya ce "Steve Mnuchin mai hada-hadar kuɗi ne da za a bugi ƙirji da shi a ko'ina cikin duniya, ma'aikacin banki ne kuma ɗan kasuwa, ya kuma taka gagarumar rawa wajen bullo da shirinmu na bunƙasa gawurtaccen tattalin arziƙi da zai samar da miliyoyin ayyukan yi."
Sai dai ba duk magoya bayan Donald Trump ne ke maraba da tunanin miƙa wa riƙaƙƙen mai hada-hadar hannayen jari a kasuwar Wall Street akalar harkokin kuɗin ƙasar.
James Mattis - Sakataren Tsaro
An bayyana janar mai murabus na rundunar zaratan sojan Amurka (Marine Corps) a matsayin babban sakataren harkokin tsaron Trump. A wani saƙon tweeter bayan ganawar James Mattis da sabon shugaban a watan Nuwamba, Trump ya bayyana tsohon sojan mai shekara 66 a matsayin wani "hamshaƙi", ya ƙara koɗa shi da: "Janar ɗin Janarorin gaske!"
Janar Mattis ya yi aiki a rundunar zaratan sojan tsawon shekara 44, ya jagoranci yaƙi a Iraki da Afghanistan.
Asalin hoton, Reuters
Gen Mattis ya yi murabus daga rundunar soji a 2013 bayan shafe fiye da shekara 40
Ya yi ƙaurin suna a kan kalamansa na gatse. An soki lamirinsa a 2005 bayan ya yi magana - kan yadda wasu maza a Afghanistan ke marin mata... saboda ba su sanya hijabi ba - cewa ai kuwa da sun fi burgewa, idan harbinsu suka yi."
John Kelly - Sakataren Tsaron Cikin gida
Ana sa ran shugaba Trump zai naɗa tsohon Janar ɗin dakarun zaratan soja don kula da harkokin tsaron cikin gida, sashen da ke da alhakin kula da harkokin tsaro masu yawa kama daga harkokin shige da fice da kutsen intanet zuwa tsaron filayen jirgin sama da ɓarkewar annoba.
Tsohon Janar ɗin mai tauraro huɗu wanda ya shafe tsawon shekara 40, ya yi ritaya a watan Janairu inda ya bar muƙaminsa na kwamandan rundunar dakarun Amurka ta kudanci, da ke kula da harkokin soja a Latin Amurka da Karebiyan.
An kashe ɗansa Robert, mai muƙamin laftana a rundunar zaratan sojin Amurka, a 2010 cikin Afghanistan.
Asalin hoton, Getty Images
Janar John Kelly ya bayar da shaida a gaban majalisar dokoki
Tom Price - Sakataren lafiya da harkokin Ɗan'adam
Ɗan majalisar wakilai daga Georgia kula likitan ƙashi ne da ya jagoranci kwamitin kasafin kuɗi a majalisar babban mai suka ne ga shirin kula da lafiya na Obamacare.
Mai shekara 62, wanda aka zaɓa karo shida zuwa majalisar wakilai yana cikin masu ba da gagarumar gudunmawa a shirin jam'iyyar Republican don wargaza tsarin lafiya na Obamacare mai rangwame.
Asalin hoton, Reuters
Trump yana yaba masa da cewa, "mai warware matsala ne da ba ya gajiya" wanda kuma "cancantarsa ta yi fice don jagorantar ƙudurinmu na sokewa da maye gurbin Obamacare.
Jeff Sessions - Attorney General
Yana ɗaya daga cikin aminan Trump na ƙut-da-ƙut tun fara yaƙin neman zaɓe. Ya bayyana Jeff Sessions wanda sanata ne daga Alabama a matsayin "mai zurfin ilmin shari'ah da za a iya taƙama da shi a ko'ina a duniya".
Mr Sessions ya ce yana "rawar jiki" ya rungumi burin Trump na "Amurka daya da kuma ƙudurinsa na samun daidaito ta fuskar adalci a wajen doka".
Asalin hoton, AFP
Mai shekara 69 ya goyi bayan mamayar da Amurka ta yi wa Iraƙi a 2003, lamarin da Trump ya ce, "wani mummunan abu ne na shiririta da aka yi".
Zarge-zargen nuna wariyar launin fata ta yi masa dumu-dumu a tsawon shekarunsa na aiki.
An zargi Mr Sessions da kiran wani mataimakin lauyan gwamnatin Amurka da suna "yaro" ya kuma bayyana Ƙungiyar tabbatar da muradan baƙaƙen fata a matsayin "ba 'yan Amurka ba" kuma "tsarin kwamunisanci ya yi musu azama."
Mike Pompeo - Daraktan CIA
An ba da sunan ɗan majalisar wakilai na jam'iyyar Republican mai tsattsauran ra'ayi don zama sabon jagoran ayyukan leƙen asiri na Amurka.
An bai wa Mr Pompeo, ɗan shekara 52, daraktan Babbar Hukumar Leƙen asirin Amurka (CIA) ko da yake, ya goyi bayan abokin takarar Trump, Marco Rubio, zaɓen fitar da gwani.
Asalin hoton, AP
Ɗan jam'iyyar Republican daga yankin Wichita a jihar Kansas, babban mai sukar yarjejeniyar da gwamnatin Obama ta ƙulla da Iran a kan shirinta na nukiliya ne.
Mike Pompeo ya kuma bayyana adawa da rufe kurkukun Guantanamo Bay.
Reince Priebus - Shugaban Ma'aikata
Mutumin da Trump ya ɗauka a matsayin jami'in kula da ma'aikatan gwamnatinsa shekararsa 44.
Asalin hoton, Reuters
A matsayinsa na shugaban kwamitin ƙasa na jam'iyyar Republican, ya kasance wani kadarko tsakanin Trump da jam'iyyarsu a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Sai dai bai taɓa riƙe wani muƙamin siyasa ba, kuma bai je kan muƙamin jami'in shiga tsakanin fadar White House da ma'aikatun gwamnati da gogewa a fannin tsara manufofi ba.
IYALI
Melania Trump
Tsohuwar mai tallata zayyanar tufafi ce kuma an haife ta ƙasar Slovenia, Melania ta auri Donald Trump a watan Janairun 2005.
Ta mara wa mijinta baya a lokacin da wani bidiyo ya bayyana yayin yaƙin neman zaɓen Trump inda yake bugun ƙirjin cewa yana cakumar mata. A watan Yulin 2016 jaridu sun yi ta yayata ta a kanun labarai bayan ta yi wani jawabi a wajen babban taron jam'iyyar Republican, inda aka zarge ta da satar jawabin Michelle Obama na 2008.
Ivanka Trump
Wataƙila ita ce mafi shahara a cikin 'ya'yan Trump, 'ya ce a wajen matarsa ta farko Ivana. Ta yi tallar zayyanar tufafi a shekarun ƙuruciyarta a yanzu ita ce mataimakiyar shugaba a cibiyar harkokin Trump.
Ɗan'uwanta Donald Ƙarami ya ce Ivanka 'yar shekara 35, 'yar lele ce, kuma mahaifinsu yana kiran ta da "'Yar baba".
Asalin hoton, AFP
Melania Trump za ta taka rawa sosai a mulkin Trump
Ta samu babban matsayi irin wanda wata cikin matan Trump ba su taɓa samu ba a harkokin kasuwancinsa, an ce ita ce za ta riƙe wasu manyan harkokin kasuwancinsa.
Ta koma addinin yahudanci bayan ta auri Jared Kushner a 2009.
Jared Kushner
Mijin Ivanka, ɗa ne ga wani fitaccen mai harkar gine-gine a New York kuma shi ne mai jaridar 'Observer' ta mako-mako tsawon shekara 10.
Tiffany Trump
'Yar Trump ce a wajen matarsa ta biyu Marla Maples. Mai shekara 23 tana da ƙalatar amfani da Twitter da Instagram.
Donald Trump Jr
Babban ɗan Donald Trump a wajen Ivana. Yanzu shi ne babban mataimakin shugaba a cibiyar kasuwancin Trump, ɗan shekara 38 yana auren Vanessa Haydon bayan mahaifinsa ya haɗa su a wani wajen bikin nuna kayan ƙyale-ƙyale.
An zarge shi tare da kaninsa Eric a kan jarabar farautar manyan namun daji bayan wasu hotuna sun bayyana inda aka nuna su kusa da wasu dabbobi da aka kashe ciki har da damisa da kada. Donald Ƙarami kuma yana riƙe da jelar wata giwa da aka cizge.