Majalisar Gambia ta tsawaita wa'adin Yahya Jammeh

Yahaya Jammeh

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Tun a shekarar 1994 Yahya Jammeh ya karbi ragamar mulki bayan ya yi juyin mulki

Majalisar dokokin kasar Gambiya ta kara wa'adin mulkin Shugaban kasar Yahya Jammeh da kwana 90.

A ranar Alhamis ne shugaban zai sauka daga mulkinsa sakamokon shan kaye da ya yi a zaben da aka gudanar a watan Disamba.

Majalisar ta kuma amince da dokar ta bacin da Shugaba Jammeh ya sanya a kasar ta kwana 90.

Rikita-rikita

A tsarin kundin mulkin Gambia ranar Alhamis ce aka sa domin rantsar da sabon zababben Shugaban kasa, Adama Barrow.

Sai dai da wannan sabon hukunci da majalisar kasar ta yanke akwai yiwuwar ba lallai a yi rantsuwar ba musamman da yake Mista Barrow yana kasar Senegal bisa shawarar da kungiyar ECOWAS ta bayar ya jira a can kafin rantsar da shi.

Tun bayan da aka yi zaben dai kasar ta shiga cikin rikicin siyasa, al'amarin da yake sanya fargaba a zukatan mutane musamman 'yan kasashen waje da yanzu haka suka fara tattara nasu-ya-nasu domin barin ta.

Ofishin kula da harkokin waje na Birtaniya ya umarci 'yan kasar da su dakatar da kai ziyara Gambia har sai abin da hali ya yi.