An katse intanet a wani yanki na ƙasar Kamaru

Cameroon Internet

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kafar intanet ke ba da damar shiga shafukan sada zumunta

Rahotanni daga jamhuriyyar Kamaru sun ce an toshe intanet a yankuna da dama musamman Bamenda, inda ake amfani da Ingilashi da fama da yawan tashin hankali.

Wani kamfanin samar da intanet na Amurka Akamai, ya ce sun lura da katsewar harkokin sadarwa a cikin daren Talata.

Shi ma wani kamfani da ke samar da layukan sadarwar intanet da kuma bibiyar tafiyar intanet ɗin ya bayar da wasu bayanai da ke nuna faɗuwar harkokin sadarwar intanet a ƙasar.

Wasu mutane sun buga saƙwannin Twitter game da katsewar intanet ɗin.

Wannan matakin dai ya biyo bayan tsawatarwa da kuma fadakarwa da Gwamnati ta yi inda take zargen cewa ana wallafa labarai marasa tushe da kuma na batanci a wadannan shafukan.

Ana fama da tunzuri a arewa maso yammacin Kamaru sakamakon yunƙurin mutanen yankin da ake amfani da Ingilishi a kan shirin ɓullo da wata doka don tilasta amfani da harshen Faransanci a makarantu da kotuna.

Rahotanni sun ce an kama jagororin yankin kafin fuskantar katsewar intanet ɗin.