A gaggauta taimaka wa 'yan Nigeria da harin soja ya jikkata

Rann, Nigeria

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Har yanzu akwai mutum 46 da suka jikkata a sansanin na Rann

Kungiyoyin ba da agaji sun yi kira da a gaggauta kwashe mutanen da jiragen yakin Najeriya suka jikkata bisa kuskure domin ba su cikakkiyar kulawa.

Hukumar agaji ta Red Cross ta ce ana yi wa mutum 46 magani kan munanan raunukan da suka ji, kwana guda bayan kai harin a sansanin 'yan gudun hijira.

Fiye da mutum 70 ne suka mutu a harin, wanda aka yi kuskuren kai wa sansanin 'yan gudun hijira a kauyan Rann a Arewa maso Gabashin kasar.

Sai dai adadin ka iya karuwa idan har wadanda suka jikkata suka ci gaba da kasancewa cikin mummunan halin da suke ciki.

Tuni wata tawagar gwamnatin tarayyar kasar ta isa birnin Maiduguri domin jaje da kuma duba wadanda lamarin ya ritsa da su.

Dr Laurent Singa, wani likita na Red Cross da ke Rann, ya ce: "Yanayin dakunan shan magani a nan ba su da kyau, don haka ya kamata a kwashe dukkan marasa lafiya zuwa Maiduguri ba tare da bata lokaci ba".

Tuni aka kwashe mutum tara zuwa babban birnin jihar ta Borno, a cewar kungiyar.

Rundunar sojin Najeriya ta nemi afuwa kan lamarin, tana mai cewa kuskuren yaki ne, amma kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta ce hakan ba zai wanke su daga daukar alhakin lamarin ba.

Sannan ta yi kira da a biya wadanda abin ya shafa diyya.

Ana kyautata zaton wannan ne karon farko da sojin Najeriya suka dauki alhakin yin kuskure a yakin da aka shafe shekara bakwai ana yi.

Sai dai mazauna kauyuka sun sha yin korafin cewa ana kashe musu jama'ar da ba sa dauke da makamai.