Me ya sa Jammeh ba ya son sauka daga mulki?
A ranar Alhamis ne ake sa ran za a rantsar da sabon shugaban Gambiya Adama Barrow, sai dai har zuwa yanzu shugaba mai barin gado, Yahaya Jammeh ya ki amincewa da shan kayen da ya yi, har ma yana ta fiddo da sabbin dokoki da za su taimaka wajen hana shi mika mulki.
To ko me ye zai kasance a ranar, ganin cewa shi ma Adama Barrow a yanzu haka yana kasar Senegal?
Mun yi duba kan dalilan da suka sa Mista Jammeh ba ya son barin mulki da kuma abin da ka iya zuwa ya dawo idan lamarin ya ci tura.
Menene amfanin dokar ta baci?
Asalin hoton, AFP
Ya Jammeh ya karbi mulki a juyin mulkin da aka yi a Gambia a shekarar 1994
Dokar ta baci da shugaban Gambiya mai barin gado Jammeh ya sanya kwana guda kafin cikar wa'adin mulkinsa ya kara jaddada aniyyar da yake da ita ta ci gaba da zama a kujerar mulki.
Shugaban Gambiyar ya ce dokar ta bacin da aka sa zata cike gibin shugabanci a yayin da kotun koli ke duba karar da ya shigar na kalubalantar sakamakon zaben da aka yi a watan Disamba.
Kotun ba zata iya sake zama ba har sai watan Mayu sakamakon rashin alkalai wadanda dole kasashen yammacin Afirka da ke makwabtaka da kasar za su samar.
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Masu sharhi sun ce matakin ya bayyana alamun cewar zai yi watsi da kokarin da masu shiga tsakani suka yi da kuma niyyarsa ta so ya cigaba da mulki bayan wa'adinsa ya kawo karshe.
Me hakan ke nufi ga nasarar Adama Barrow?
Kafin a kafa dokar ta bacin, Adama Barrow wanda ke Senegal makwabicyar kasarsa, yace za a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a ranar Alhamis a Gambia.
Da Adama Barrow zai sha rantsuwa ne a filin wassani da ke Bakau amma, gannin irin takun Mista Jammeh, dole ne ya kasance babu wani tabbas a tare da wannan shirin.
Ba a kuma ce komai ba a kan wanda zai jagoranci rantsar da shi - dama an saba babban alkalin kasar ne yake rantsar da shugaban kasa amma lauyoyi na cewa, a tsarin dokar Gambiya wannan ba lallai bane kuma ko kwamishina zai iya rantsar da shugaban kasar.
Yaya 'yan Gambia ke ji game da lamarin?
Mutane na cikin tararradi a Banjul babban birnin Gambiya, a kan yiwuwar ruruwar rikicin siyasa. Dakarun tsaro masu dauke da makamai na tsaron wuraren da ake binciken ababen hawa a birnin.
Dubban mutane sun tsere zuwa kasashen da ke makwabtaka ko kuma kauyuka saboda tsoron yiwuwar barkewar rikici. Kafin dokar ta bacin da aka kafa, masu goyon bayan Mista Barrow sun bukaci 'yan Gambiya da su "bi ka'idojin doka kuma kar su kula masu tsokana".
Wakilin BBC, Umaru Fofana, wanda ke Banjul din yace a tsorace mutene suke. Mutane sun tanadi abinci da ruwa. ''Kowa na addu'a domin a warware takaddamar cikin lumana,'' in ji Fofana.
Menene matsayin Jammeh?
Mista Barrow na Senegal
Da farko dai Mista Jammeh wanda ya karbi mulki a juyin mulkin shekarar 1994, ya amince da nasarar da Mista Barrow ya yi a zaben amma kuma daga bisani ya sauya matsayinsa ya ce ba zai sauka daga kan mulki ba.
Mista Jammeh ya shigar da kara a kotun koli, inda ya kalubalanci sakamakon zaben kuma yace hakan na nufin a tsarin mulkin kasar Mista Barrow ba zai iya hawa mulki ba.
Me yasa Jammeh baya so ya sauka daga kan mulki?
Mista Jammeh ya ce akwai abubuwan da aka yi ba dai-dai ba a zaben, ciki har da korar wasu masu goyon bayansa daga rumfunan zabe da kuma kurakurai da hukamar zabe ta yi.
Hukumar ta amince cewar akwai kurakurai a sakamakon da ta fara fitarwa , amma kuma ta ce Mista Barrow ne ya lashe zaben.
Mista Jammeh ya ce zai ci gaba da zama kan karagar mulki har sai an sake wani sabon zabe.
Sannan masu sharhi na ganin irin salon mulkin da Jammeh ya yi da ya yi kama da na kama karya, ya taka duk wanda ya so, na daga cikin dalilan da yasa ba ya son sauka daga mulkin.
Wasu kuma na ganin akwai batun yin almundahana da kudin gwamnati wanda da zarar ya sauka shugaban da zai hau zai iya tuhumarsa da hakan.
To sai masu sharhi na ganin duk dadewar da zai yi a kan mulkin dole wata rana ya sauka, kuma saukarsa a yanzu cikin salama na iya sa sabon shuagaban ya kyale shi kan duk wani abu da yake ganin ya yi mara kyau.
Ya abokansa suka mayar da martani?
Ministocin Jammeh na ci gaba da kauracewa gwamnatinsa. A ranar Talata ne dai hudu daga cikin 'yan majalisarsa wadanda suka hada da ministocin kudi da na harkokin waje suka yi murabus, tare da wasu biyu, wadanda suka yi murabus a makon da ya gabata a kan kin amincewa da kayen da ya sha.
Me ke faruwa a kotun kolin?
Asalin hoton, AFP
Mista Barrow ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a watan Disamba a Gambia
An hayi alkalai daga kasashen Najeriya da Saliyo domin su saurari karar da aka shigar su kuma sauya sakamakon zaben, amma basu isa Banjul ba.
Emmanuel Fagbenle, babban alkalin Gambiya, ya ce kotun zata sake zama a cikin watan Mayu kuma mai yiwuwa har sai watan Nuwamba saboda Onogeme Uduma, dan Najeriya wanda zai kasance a matsayin shugaban kotun, yana da ayyukan da zai yi a watanni masu zuwa.
Wane martani kasashen makwabtaka ke bayarwa?
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, Ecowas ta yi kokarin shawo kan mista Jammeh ya sauka daga kan mulki amma ba ta yi nasara ba.
Bayanai daga yankunan Afirka ta yamma na cewa ana tunanin a yi amfani da karfi wajen cire shi a kan kujerar. Kasashen yammacin Afirka za su tura sojojinsu domin kau da shi daga kan mulki idan har Jammeh bai sauka ba kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wata majiyar dakarun rundunar sojin Najeriya na cewa.
Reuters ta ambato wata majiya a rundunar sojin Najeriyar na cewa, "An yanke shawarar ba zai ci gaba da kasancewa shugaban kasar Gambiya ba a lokacin da wa'adinsa ya kare.''
Ta ya za a shawo kan takaddamar?
Asalin hoton, Thinkstock
Mutane da dama wadanda ba 'yan Gambia ba ne na kallon kasar a matsayin kasar da 'yan yawon bude ido ke so kwarai
Mista Barrow ya nisanta kansa daga martanin da 'yan adawa ke yi, inda suke cewa mai yiwuwa a yi zargin Mista jammeh da amfani da mukaminsa ba bisa ka'ida ba.
Ya ce Mista Jammeh zai iya ci gaba da zama a Gambiya kuma za a karramashi kuma a bashi duka wata dama ta tsoffin shugabannin idan har ya sauka.
Sai dai masu sharhi sun ce ba lallai bane kalaman sulhu da abokan adawansa suke amfani da shi ya iya shawo kan Jammeh.
Wata dama kuma da majalisar Najeriya ta bai wa Mista Jammeh ita ce ta bashi mafakar siyasa a wata kasar a Afirka.