Wata ta watsa wa wanda za ta aura asid a Indiya

Lydia Yeshpaul

Asalin hoton, BANGALORENEWSPHOTO

Bayanan hoto,

Lydia Yeshpaul ma'aikaciyar jinya ce

A wani lamari da ba kasafai ake samun aukuwar irinsa ba, wata matashiya 'yar shekara 26 ta watsawa wanda za ta aura asid a garin Bangalore da ke India.

Lydia Yeshpaul ta bayyana a wata kotu da ke Bangalore ne bayan an tuhume ta da wannan laifi.

Ana zarginta da watsa asid din a fuskar Jayakumar Purushottan da kuma yunkurin kashe shi.

Mista Purushottam ya ce iyayensa ba su amince da aurensu da yarinyar ba a kan dalilai na addini.

Wani babban jami'in 'yan sanda ya shaida wa BBC cewa wannan ne karon farko da ofishin 'yan sanda na wannan yankin ya fuskanci irin wannan lamarin na a samu wata da watsawa wani acid.