Kun san sau nawa Trump ya jawo ce-ce-ku-ce?

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ya zargi matar Obama da cewa bata iy komai ba sai yakin neman zabe

BBC ta yi nazari ta kuma zakulo wasu daga cikin irin kalaman da Donald Trump ya yi a lokutan yakin neman zabe wadanda suka jawo a ka yi ta sharhi a kai, da kuma irin tasirin da watakila za su iya yi bayan ya dare kujerar mulkin.

"Zan hana musulmai shiga Amurka"

Donald Trump ya yi kiran da a hana Musulmai shiga kasar Amurka kwata-kwata tun ma kafin ya tsaya takara a karkashin jam'iyyar Republican.

Mista Trump ya bayyana cewa wani sakamakon jin ra'ayoyin mutane ya nuna cewa Musulmai da yawa ba sa son Amurka, kuma ya kamata a kare mutanen kasar daga barazanarsu har sai an gano dalilin da ya sa Musulmai suka tsani kasar.

Zababben shugaban Amurkan ya kara da cewa ya kamata gwamnatin Amurka ta rika sa ido a Masallatai domin sanin me ake gudanarwa a cikinsu.

Mista Trump dai ya yi wadannan kalamai ne kwanaki kadan bayan wani mutum da matarsa sun kashe mutane 14 a birnin California.

A lokacin hukumar tsaro ta FBI ta ce mutanen da suka bude wutar, masu tsatsaurar akidar musulunci ne.

Wadannan kalamai nasa sun jawo mayar da martani daga kasashen duniya daban-daban har da wadanda ba na musulmai ba.

"Zan gina katanga tsakanin Amurka da Mexico"

Asalin hoton, Donald Trump tare da shugaban Mexico, Enrique Pena

Bayanan hoto,

Donald Trump ya ce dole ne a katange Amurka daga Mexico.

Shi dai Donald Trump ya soki 'yan ci rani 'yan kasar Mexico da ke Amurka, a lokacin yakin neman zabensa, a inda ya sha alwashin gina doguwar katanga tsakanin kasashen biyu.

Donald Trump ya fadi kalaman ne a lokacin da yake jadadda aniyyarsa ta hana baki 'yan ci-rani shiga kasar da zarar ya zama shugaban kasa.

Mista Trump ya bayyana kalamansa ne a wani jawabin amincewa da tsayar da shi takara da jam'iyyarsa ta yi.

"Dole kungiyar tsaro ta NATOta biya haraji a kan tsaron da Amurka ke bata"

Bayanan hoto,

Mista Trump zai matsawa NATO lambar janye dakarun su daga iyakar kasar Rasha

Mista Trump ya ce zai sake nazari kan yiwuwar taimaka wa kasashe kawayen Amurka da aka kai wa hari idan har ba a biya abubuwan da suka zama hakki kasar ta biya ba a cikin kawancen NATO.

A lokacin sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO, ya gargadi zababben shugaban Amurka Donald Trump cewa matakin da yake shirin dauka kana dangatakar da ke tsakanin Amurka da Tarayyar Turai bai dace ba.

Mista Jens Stoltenberg ya yi wannan kalami ne a jaridar Observer ta Birtaniya, inda ya kara da cewa kasashen yammacin duniya na fuskantar kalubalen tsaro da aka dade ba a ga irin sa ba.

"Dole mu hana Larabawa kwarara cikin Amurka"

Donald Trump dai ya lashi takobin kakkabe 'yan ta'adda daga Amurka, wadanda suke da tsaurin akida.

Shugaban Amurkan mai jiran gado ya ce, "wasu mutane da ba a san asalinsu ba suna kwararowa daga gabas ta tsakiya, saboda haka dole ne mu dakatarsu".

''Sai na daure Hillary Clinton''

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hillary ce wadda ta fafata da Trump a neman takarar shugabancin Amurka ta sha kaye

Donald Trump ya kuma sha alwashin sai daure abokiyar takararsa ta jam'iyyar Democrat Hillary Clinton a lokacin da suke kamfe.

Shi ma wannan batu ya janyo ce-ce-ku-ce a duniya.

Sai dai kuma daga baya ya yi watsi da tsauraran alkawuran da ya yi lokacin yakin neman zabe ciki har da na batun daure Hillary din.

A cikin wata doguwar hira da jaridar New York Times, Mr. Trump ya ce ba zai so ya bata wa iyalin Clinton rai ba, yana mai cewa shi yana son ya manta abin da ya wuce baya ne.

Sai dai duk da wadannan ikirari da kalamai da ya sha yi, masu sharhi suna ganin manufofin kasashen wajen Amurka ba za su bar Mista Trump ya yi gaban kansa wajen gurbata mu'amalar kasar da sauran kasashe ba, don haka babu wani tasiri da za su yi.

Yanzu dai duniya ta sa ido don ganin irin kamun ludayin Donald Trump da yadda zai gudanar da mulkinsa bayan ya sha rantsuwar kama mulkin a ranar Juma.