Jikin tsohon shugaban Amurka Bush ya tsananta

George H. W. Bush (babba)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shekarun Bush babba na haihuwa 92.

An mayar da tsohon shugaban Amurka, George Bush, babba, wanda ya dade a asibitin Texas tun ranar Asabar, bangaren kula da wadanda rashin lafiyarsu ta tsananta.

An dai ce yana cikin hayyacinsa tun bayan da aka yi masa maganin cutar sanyin hakarkari ta nimoniya (Pneumonia).

Ita ma mai dakinsa, Barbara tana kwance a asibitin da mijin nata yake domin kula da ita a matsayin riga-kafi saboda gajiya.

Tsohon shugaban na da shekara 92 a duniya.

A lokacinsa ne Amurka ta kaddamar da yaki kan kasar Iraki a shekarun 1990.

Dansa Bush karami, ya zama shugaban kasar ta Amurka daga bisani, inda ya jagoranci yaki kan kasar ta Iraki a karo na biyu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bush babba a lokacin da ya yi bikin cikarsa shekara 90, inda ya yi saukar lema