Barrow zai sha rantsuwar kama aiki a Senegal

Barrow

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Barrow ya taba zama mai gadi a wani kanti da ke London

Zababben shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya ce zai sha rantsuwar kama aiki a ofishin jakadancin kasar da ke Senegal.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mr Barrow ya ce za a rantsar da shi da misalin karfe hudu na yamma a agogon kasar.

Sai dai rahotanni na cewa hukumomin Gambia sun rufe ofishin jakadancin kasar da ke Senegal.

Barrow dai ya je kasar ta Senegal ne tare da wakilan kungiyar kasashen raya tattalin arzikin yammacin Afirka, ECOWAS, wadanda suka hada da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, bayan yunkurin da kungiyar ta yi na ganin Yahya Jammeh ya sauka daga mulki cikin ruwan-sanyi ya gagara.

A ranar Laraba ne dai wa'adin Jammeh a kan mulki ya kare, koda yake majalisar dokokin kasar ta tsawaita zaman sa a kan mulki zuwa kwana 90.

ECOWAS ta sha alwashin yin amfani da karfin soji domin kawar da shi daga mulki.

Tuni dai 'yan kasar da ma 'yan kasashen waje da ke yawon bude ido a kasar suke ficewa daga kasar saboda tsoron barkewar rikici.

Barrow ya kayar da Mista Jammeh a zaben da aka yi a watan Nuwamba.

Da farko dai Jammeh ya amince da shan kaye sannan ya taya Mista Barrow murna, amma daga bisani ya ce ba zai sauka daga mulki ba saboda zargin da ya yi cewa an tafka kura-kurai a zaben.

Ya kuma garzaya kotu inda yake kalubalantar sakamakon zaben.