Mutane da dama sun mutu sakamakon dusar kankara

Matukin motan asibiti a yakin Campotosto na fama da kankara

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Girgisar kasa ta yi sanadiyar dusar kankara a Italiya ta tsakiya ranar Laraba

Wani jami'i a Italiya ya ce mutane da dama sun mutu a otal din Rigopiano sakamakon zubar dusar kankara.

Masu aikin ceto sun ce fiye da mutane 30 ne ba a gani ba zuwa yanzu bayan da dusar kankara ta lullube otal din da ke tsakiyar birnin Italiya.

Dusar kankarar ta zubo ne sakamakon wata girgizar kasa da ta faru a ranar Laraba.

Masu aikin ceto sun yi ta isa otal din Rigopiano domin kokarin ceto wadanda abin ya ritsa da su.

Sai dai dusar kankarar ta lullube hanyar isa wajen, al'amarin da yasa masu aikin ceton shan fama.

An ciro gawar wani mutum daya da ya rasa ransa daga karkashin dusar.

Haka kuma an gano wasu mutane biyu da ransu wadanda kankarar ta rufe su.