Buhari zai tafi hutun kwana goma don ganin likita

Buhari da Osinbajo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A wancan lokacin Osinbajo ne ya ja ragamar Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi hutun kwana goma wanda ake yi shekara-shekara.

Shugaban majalisar dattawan kasar Bukola Saraki ne ya sanar da hakan a wasikar da ya karanta a zauren majalisar ranar Alhamis.

Saraki ya ce Shugaba Buhari zai tafi hutun ne ranar 23 ga watan Janairu sannan ya dawo ranar shida ga watan Fabrairu.

Shi ma shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa zai tafi Birtaniya ranar Alhamis a matsayin wani bangare na hutun kwana goman da zai yi

A cewar sa mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ne zai tafiyar da al'amuran kasa idan ya tafi hutun.

Ba wannan ne karon farko da shugaban kasar ya aike da wasika ga majalisar dattawa inda yake sanar da ita aniyarsa ta tafiya hutu ba.

A watan Fabrairun shekarar 2016, Mista Buhari ya yi gajeren hutu na kwana biyar.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya gudanar da ayyukan shugaban kasar bayan tafiyar sa hutun.