Nigeria: 'Yan sanda sun saki mawallafin jaridar Premium Times

Premium Times raided

Asalin hoton, PREMIUM TIMES

Bayanan hoto,

Jami'an sun ce suna gudanar da bincike a kan ƙorafin da rundunar sojan ƙasar ta shigar kan jaridar

Kafar yada labarai ta Premium Times ta ce 'yan sandan Nigeria sun saki mawallafinta bayan da suka yi dirar mikiya a ofishin jaridar da ke Abuja, babban birnin kasar, suka kama shi, tare da wata ma'aikaciya.

Wata majiya ta jaridar ta tabbatar wa BBC cewa 'yan sandan sun saki jami'an biyu bisa sharadin cewa mutanen biyu za su sake kai kansu wurin 'yan sandan a ranar Juma'a.

Tun da farko dai jaridar ta wallafa a shafinta cewa 'yan sanda sun kama Dapo Olorunyomi da wata wakiliyar jaridar, Evelyn Okakwu, a lokacin samamen a yammacin ranar Alhamis, inda suka kwashe wasu takardu.

Ta kara da cewa 'yan sandan, wadanda suka je a fararan kaya, sun ce sun je ne kan wani korafi da babban hafsan sojan kasar, Laftanar Janar Tukur Buratai ya yi.

Jaridar dai na takun-saka da rundunar sojin Najeriya, wacce ta zarge ta da wallafa rahotannin karya kan sojojin da kuma shugabansu Janar Buratai.

Ita dai Premium Times ta musanta zargin, sannan ta nemi jami'an sojin da su nemi afuwa kuma su daina yi mata barazana.

Wani babban jami'i a jaridar ya shaida wa BBC cewa sun yi mamakin sumamen saboda sojojin sun ce sun kai su kotu, a don haka tuni suka fara shirin kare kansu a gaban kuliya.

Wannan lamari zai sa shakku kan yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ke daukar batun 'yancin fadar albarkacin baki da kuma hakkin dan'adam.

Sumamen dai ya zo ne 'yan kwanaki bayan jaridar ta ƙi amincewa da buƙatar rundunar sojan ƙasar da ke neman ta janye wasu labarai da ta buga a kan sojan ƙasar da abubuwan da suke yi.

Kawo yanzu rundunar 'yan sandan da ta sojojin kasar ba su ce komai game da lamarin ba.