An rantsar da Adama Barrow shugaban Gambia

Barrow

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Barrow ya taba zama mai gadi a wani kanti da ke London

Adama Barrow ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban ƙasar Gambia a ofishin jakadancin kasar da ke Senegal.

Shugaban kungiyar lauyoyi ta Gambia Sheriff Tambadou ne ya rantsar da shi.

A yanzu kasar na da mutum biyu da ke ikirarin kasancewa shugabanninta.

Mista Barrow ya je Senegal ne bayan yunkurin da kungiyar Ecowas ta yi don ganin Yahya Jammeh ya sauka daga mulki cikin ruwan-sanyi ya gagara.

Jawabin kama-aiki

A jawabinsa na farko don kama mulki Shugaba Adama Barrow ya ce: "Daga yau (Alhamis), Ni ne shugaban ƙasar Gambia ko ka/kin zaɓe ni ko ba ka/ki zaɓe ni ba."

Ya ce "Wannan nasara ce ga ƙasar Gambia.. mulki a hannun jama'a yake a Gambia"

A cewarsa "Wannan rana ce wadda babu wani ɗan Gambia da zai taɓa mantawa da ita... karon farko tun bayan samun 'yancin kai, Gambia ta sauya gwamnati ta hanyar ƙuri'a".

Asalin hoton, RTS

Shugaban ƙasa biyu

A ranar Laraba ne wa'adin Yahya Jammeh a kan mulki ya ƙare, ko da yake majalisar dokokin ƙasar ta tsawaita zamansa a kan mulki da kwana 90.

Senegal ta ba shi zuwa tsakar daren ranar Talata domin ya sauka, ko kuma ta afka masa.

Tuni dakarun kasar da na Najeriya da Ghana suka isa kan iyakar Gambia domin shirin kifar da Mista Jammeh da zarar sun samu izini.

Kuma rahotanni sun ce jirgin yakin Najeriya ya yi shawagi kan sararin samaniyar kasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Adama Barrow ya samu goyon bayan matasa sosai

ECOWAS ta ɗauki alwashin yin amfani da ƙarfin soja don kawar da Jammeh daga kan karagar mulki.

'Yan Gambia da ma 'yan kasashen waje da ke zuwa yawon bude ido a kasar da yawa ne suka fice zuwa wasu ƙasashe maƙwabta saboda tsoron ɓarkewar rikici.

Barrow ya kayar da Mista Jammeh a zaben da aka yi cikin watan Disamba.

Da farko dai Jammeh ya amince da shan kaye sannan ya taya Mista Barrow murna, amma daga bisani sai ya ce ba zai sauka daga mulki ba saboda zargin da ya yi cewa an tafka kura-kurai a zaben.

Ya kuma garzaya kotu inda yake kalubalantar sakamakon zaben.