Mexico: An tasa keyar Guzman mai safarar kwaya zuwa Amurka

Joaquín "El Chapo" Guzman a hannun jami'an tsaro

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Kawo yanzu ba a san inda aka nufa da Joaquín "El Chapo" Guzman ba a Amurka

An tasa keyar kasurgumin mai hada-hadar miyagun kwayoyin nan dan Mexico Joaquín "El Chapo" Guzman, zuwa Amurka, kamar yadda gwamnatin kasarsa ta tabbatar a ranar Alhamis.

Kafofin yada labarai na kasar ta Mexico sun ruwaito cewa an dauki Guzman ne daga filin jirgin saman Ciudad Juarez.

Amurka na neman Mista Guzman ne bisa zargin satar shigar da tarin miyagun kwayoyi kasar.

Ana neman shugaban kungiyar da ake kira Sinaloa wadda ke hada-hadar miyagun kwayoyin ne a jihohin Amurka biyu.

Daya daga California, sannan kuma dayan, a Texas, inda zai iya fuskantar hukuncin kisa.

A baya Mista Guzman ya taba tserewa daga gidajen yari biyu masu tsananin tsaro, na Mexico.