Umra: 'Yan Birtaniya 6 sun rasu a Saudiyya

Wasu daga cikin iyalan da suka rasu a hadarin

Asalin hoton, FAMILY HANDOUT

Bayanan hoto,

Daga hagu; Khurshid Ahmed, Talat Aslam, Mohammed Aslam, Rabia Ahmad, Noshina Ahmed da jariri ; Adam, dukkansu sun mutu a hadarin

Wasu 'yan Birtaniya shida sun rasu a wani hadarin mota a Saudi Arabia, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Madina, yayin aikin Umra.

Ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya wadda ta tabbatar da lamarin ta ce, mutanen wadanda suka hada da wani jariri, sun rasu ne sakamakon faduwar da motarsu ta yi saboda fashewar taya, a ranar Laraba.

Hudu daga cikinsu, dangi ne daga Manchester, sannan kuma da mata da miji daga Glasgow.

Mahaifiyar jaririn na daga 'yan Umrar hudu daga Birtaniya, wadanda suka ji rauni a motar bus din, wadda take dauke da mutane 12.

Asalin hoton, FAMILY HANDOUT

Bayanan hoto,

Ma'aurata Noshina da Khurshid Ahmed tare da jikansu (jariri) na daga wadanda suka rasu a hadarin

Kamfanin safarar mahajjata na Haji Tours da ke Manchester, wanda ya yi jigilar mutanen ya ce sunan jaririn da ya rasu Muhammad Adam Anis, wanda dan wata biyu ne.

Kamfanin ya kuma ce kakannin jaririn na daga wadanda suka rasa ransu, namijin Khurshid Ahmed mai shekara 64 da matarsa Noshina Ahmed, mai shekara 49, da kuma yayarta Rabia Ahmad, mai shekara 57.

Kamfanin safarar mahajjatan ya ce ya ce ya shirya kai 'yan uwan mamatan daga Landan zuwa Saudi Arabia ranar Alhamis da yamma.

Miji da matar da hadarin ya hallaka kamar yadda hukumomin babban masallacin Glasgow suka bayyana, sun ce sunansu Mohammad Aslam da Talat Aslam, wadanda suke da 'ya'ya biyar.

Daga cikin wadanda suka samu raunuka har da wata mata mai shekara 63, wadda ke cikin mawuyacin hali.

Ita kuwa mahaifiyar jaririn da ya rasu mai suna Ataka Anis da 'ya'yanta biyu, 'yan shekara biyu da hudu, suna cikin hayyacinsu, kamar yadda kamfanin ya tabbatar.

Asalin hoton, FAMILY HANDOUT

Bayanan hoto,

Khurshid Ahmed da jikansa Adam, wanda aka haifa a watan Nuwamba, sun mutu a kan hanyarsu ta zuwa Madina

Kusan mutane 7,800 ne suka mutu a hadarin mota a Saudi Arabia a shekarar 2013, kamar yadda bayanan 'yan sanda suka nuna in ji hukumar lafiya ta duniya.

Alkaluman sun nuna cewa 'yan kasar Saudiyya sama da 27 daga cikin 100,000 suka rasu a hadarin mota a shekara daya.

A Birtaniya kuwa kusan mutum uku ne daga cikin 100,000 da suka mutu a Birtaniya a hadarin mota a shekara daya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dukkanin mutanen sun rasu ne a kan hanyarsu ta zuwa Masallacin Manzon Allah (SAW)