Ta yaya Jammeh zai bar fadar gwamnatin Gambia?

Adama Barrow (left) during his swearing in ceremony

Asalin hoton, RTS

Bayanan hoto,

Mista Barrow ya nemi sojojin Gambia su zauna a barikokinsu bayan rantsar da shi

Kungiyar ECOWAS ta ce ta dakatar da sojojin Senegal daga shiga kasar Gambia, domin bayar da damar sake tattaunawa da Yahya Jammeh, mutumin da yaki sauka daga mulkin kasar bayan wa'adinsa ya kare.

Mai magana da yawun Kungiyar ta ECOWAS Mercel de Souza ya ce, an bai wa Yahya Jammeh har zuwa karfe 12 na ranar Jumma'a da ya sauka daga kujerar shugabancin kasar.

Sai dai kuma har kawo yanzu Mista Jammeh bai ce uffan ba.

Da yammacin ranar Alhamis ne dai dakarun kasar Senegal suka shiga Gambiyar domin tabbatar da cewa Adama Barrow ya karbi mulki a matsayin sabon shugaban kasar.

Hakan ya faru 'yan sa'o'i kadan bayan da Mr Barrow ya sha rantsuwar kama aiki, a ofishin jakadancin kasar da ke Dakar babban birnin Senegal.

Tuni dai kasashen duniya suka amince da shi.

Amma Yahya Jammeh wanda ya dade yana kan mulki ya ki sauka, kuma majalisar dokoki na mara masa baya.

Kasashen yammacin Afirka sun yi barazanar cire shi da karfin tuwo, yayin da ita ma Majalisar Dinkin Duniya ta amince da Mista Barrow.

Kasashe mambobin kwamitin sulhu na majalisar sun goyi bayan amfani da karfi amma sun ce, "matakin siyasa za a fara bi da farko".

Tuni dai kungiyar Ecowas ta tura shugaban kasar Guinea a matsayin wanda zai jagoranci tattaunawar sulhu da Mista Jammeh don ganin ya bar fadar gwamnatin cikin ruwan sanyi.

Shugaban hukumar Ecowas, Marcel Alain de Souza, ya ce idan har Jammeh bai bayar da hadin kai ba a tattaunawar to dole a dauki matakin soji a kansa.

Mai magana da yawun dakarun Senegal Kanar Abdou Ndiaye ya shaida wa kafafen yada labarai cewa dakarunsu sun shiga Gambia ranar Alhamis da yamma.

Tuni dakarun kasar da na Najeriya da Ghana suka isa kan iyakar Gambia domin shirin kifar da Mista Jammeh da zarar sun samu izini.

Kuma jirgin yakin Najeriya ya yi shawagi kan sararin samaniyar kasar, kuma za su iya kai hari, a cewar mai magana da yawunsu Ayodele Famuyiwa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dakarun Senegal na daga cikin wadanda suka fi kwarewa a Afirka

Jawabin kama-aiki

A jawabinsa na farko don kama mulki Shugaba Adama Barrow ya ce: "Daga yau (Alhamis), Ni ne shugaban ƙasar Gambia ko ka/kin zaɓe ni ko ba ka/ki zaɓe ni ba."

Ya ce "Wannan nasara ce ga ƙasar Gambia.. mulki a hannun jama'a yake a Gambia"

A cewarsa "Wannan rana ce wadda babu wani ɗan Gambia da zai taɓa mantawa da ita... karon farko tun bayan samun 'yancin kai, Gambia ta sauya gwamnati ta hanyar ƙuri'a".

Shugaban ƙasa biyu

A ranar Laraba ne wa'adin Yahya Jammeh a kan mulki ya ƙare, ko da yake majalisar dokokin ƙasar ta tsawaita zamansa a kan mulki da kwana 90.

'Yan Gambia da ma 'yan kasashen waje da ke zuwa yawon bude ido a kasar da yawa ne suka fice zuwa wasu ƙasashe maƙwabta saboda tsoron ɓarkewar rikici.

Barrow ya kayar da Mista Jammeh a zaben da aka yi cikin watan Disamba.

Da farko dai Jammeh ya amince da shan kaye sannan ya taya Mista Barrow murna, amma daga bisani sai ya ce ba zai sauka daga mulki ba saboda zargin da ya yi cewa an tafka kura-kurai a zaben.

Ya kuma garzaya kotu inda yake kalubalantar sakamakon zaben.