Wani direba ya kade mutane da mota da gangan a Australia

Australia Melbourne

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yansanda sun ce direban ya yi garkuwa da wata mata a cikin motar

'Yan sanda a Melbourn a kasar Astralia sun ce mutane uku ne da suka hada da karamin yaro suka mutu, bayan da wani mutum ya bi ta kansu da mota da gangan.

Sun kuma ce mutane a kalla mutum 29 ne suka samu raunuka, ciki har da wani jariri da ke cikin mummunan hali.

Motar ta bi ta kan masu tafiya da kafa ne a wani rukunin shaguna na Bourke St Mall, wani wurin saye da sayarwa mai taruwar jama'a.

'Yan sandan sun ce Police sun yi wa motar karo, kana suka harbi direban a kafada kafin su cafke shi.

Jami'an sun ce lamarin ba shi da nasaba da ta'addanci, amma mutumin mai shekaru 26 wanda ke da tarihi kan cin zarafin iyalansa, ya daba wa wani wuka da safiyar Juma'a a Kudu maso Gabashin Melbourn.

Wani faifan bidiyo a kafar yada labaran yankin ya nuna wata mota mai launin ja na tafiya tana ta sha-tale-tale a kusa da tashar jirgin titin Flinders.

'Yan sandan sun ce direban ya yi garkuwa da wata mata a cikin motar.

Wata ganau ta shaidawa BBC cewa ta ga wasu masu tafiya da kafa na kokarin kaucewa motar a lokacin da ta bi inda suke tafiya.