Nigeria: 'Yan Biafra na zanga-zangar goyon bayan Trump

Biafra

Asalin hoton, Biafra Radio

Bayanan hoto,

'Yan Biafra na sa ran samun goyon bayan Mista Trump

Rahotanni daga jihar Rivers da ke Kudancin Najeriya na cewa daruruwan 'yan aware na Biafra sun yi zanga-zanga a birnin Fatakwal.

Zanga-zangar ta nuna goyon baya ga sabon Shugaban Amurka, Donald Trump ta rikide zuwa ta abin da suka kira kawo karshen mulkin danniya a Najeriya, tare da bukatar a barsu su balle.

Bayanai sun nuna cewa an samu arangama tsakanin 'yan Biafran da kuma jami'an tsaro, har wasu sun jikkata.

Kawo yanzu BBC bata samu martani daga rundunar soji ko 'yan sandan kasar ba.

'Yan Biafra na sa ran samun goyon bayan Mista Trump, kuma sun nuna masa goyon baya tun lokacin da yake yakin neman zabe bayan da ya goyi bayan ballewar Birtaniya daga Tarayyar Turai.

Hotunan da masu fafutikar suka wallafa a Twitter sun nuna masu zanga-zangar na dauke da kyallaye da ke dauke da hoton Mista Trump da kuma jagoran kungiyarsu ta IPOB, Nnamdi Kanu.

Haka kuma sun yi ta wallafa hotunan yadda zanga-zangar tasu take kasancewa a shafin Twitter na IPOB.

Suna ta ihun cewa, ''Karshen mulkin kama-karya ya zo da kuma kirkirar jamhuriyyar Biafra".

Ba wannan ne karo na farko da 'yan Biafra ke arangama da jami'an tsaron Najeriya ba.

Ko a bara kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun zargi 'yan sanda da kashe gwamman masu zanga-zanga, zargin da suka musanta.